fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Filato

Gobara ta lalata kayyaki na miliyoyin naira a kasuwar Doya a yankin Filato

Gobara ta lalata kayyaki na miliyoyin naira a kasuwar Doya a yankin Filato

Tsaro, Uncategorized
Kayayyakin abinci da wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin nairori sun lalace sakamakon wata gobara da ta tashi a sanannen Kasuwar Doya ta Yamu a karamar hukumar Quaan Pan da ke jihar Filato a daren Lahadi. Wani mazaunin yankin, Alhaji Kabiri Buba, ya ce yawancin manoma da ‘yan kasuwa yanzu haka suna kirga asarar da suka yi. Buba ya ce, "Manoma da 'yan kasuwa sama da 100 matsalar ta shafa". Ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta taimaka wa manoma da ‘yan kasuwa. Dangane da lamarin, Sanatan da ke wakiltar Filato ta Kudu, Nora Dadu’ut a ranar Litinin ya yi ta’aziyya tare da babban basaraken yankin, Long Jan na Namu mai martaba, Alhaji Safiyanu Allahnana da sauran al’ummar musamman wadanda abin ya shafa. A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka yi gob...
Da Duminsa:Kotun Koli ta tabbatarwa Tsohon Gwamnan Filato, Dariye daurin shekaru 10 bisa satar sama da Biliyan 1

Da Duminsa:Kotun Koli ta tabbatarwa Tsohon Gwamnan Filato, Dariye daurin shekaru 10 bisa satar sama da Biliyan 1

Siyasa
Alkalai 5 na kotun koli sun tabbatarwa da tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye hukuncin daurin shekaru 9 saboda cin amanar mutane da kuma laifi.   Hukumar EFCC ta maka Tsohon gwamnan a Kotu inda take zarginsa da wawushe wasu kudin ayyukan jihar Filato da suka kai Naira Biliyan 1.126.   A shekarar 2018, babbar Kotun Tarayya ta yanke masa hukuncin shekaru 14 a gidan yari, amma daga baya kotun daukaka kara ta rage masa shekarun zuwa 10.   Ya rike mukamin gwamnan Flato daga shekarar 1999 zuwa 2007. In June 2018, Adebukola Banjoko, a judge of a Federal Capital Territory (FCT) High Court in Gudu, sentenced Dariye to 14 years imprisonment having found him guilty on 15 out the 23 counts preferred against him. However, the Court of Appeal in Abuja in...
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan fashi 3 a Filato

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan fashi 3 a Filato

Tsaro
Rundunar Sojojin Operation Safe Heaven ta sanar da kashe 'yan Fashi 3 a jihar Filato.   Kwamandan Rundunar, Janar Chukwuemeka Okonkwo ne ya bayyana haka a yau, Alhamis inda yace an kashe 'yan fashinne a daren jiya yayin da suke fashi a daidai Sansanin horas da matasa 'yan Gudun Hijira a Mangu dake garin   Yace wasu 3 kuma sun tsere da raunukan Bindiga. “The robbers had robbed three vehicles of their belongings including phones and other valuables.   “After a long pursuit by our men, three out of the six robbers  were neutralised while three others escaped and suspected to have fled into the adjoining villages with gunshot wounds,” he said.
Sakamakon gwaji ya nuna cewa Gwamna Jihar Filato, Simon Lalong ya kamu da cutar COVID-19

Sakamakon gwaji ya nuna cewa Gwamna Jihar Filato, Simon Lalong ya kamu da cutar COVID-19

Siyasa
Dakta Makut Macham, Daraktan yada labarai da hulda da jama'a na gwamnan, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Jos.   A cewar Macham, ci gaban ya biyo bayan gwajin COVID-19 da aka gudanar akan gwamnan da dangin sa. Ya ce a halin yanzu Gwamnan ya killace kansa , ya kara da cewa gwaji da akayi wa danginsa ya nuna cewa basu kamu da cutar COVID-19 ba.   Macham yace a sakamakon haka, daga yanzu gwamnan zai yi aiki daga gida a tsawon lokacin jinyarsa.   Kuma duk al'amuran jihar da ke bukatar kasancewar gwamnan a zahiri mataimakinsa zai kula da su.
An kashe mutum 2 a kasuwar kugiya dake jihar filato

An kashe mutum 2 a kasuwar kugiya dake jihar filato

Uncategorized
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Filato ta tabbatar da kisan wasu mutane biyu a kasuwar Kugiya da ke Bukuru, karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar.   ASP Ubah Ogaba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi a Jos. Ogaba ya ce lamarin ya haifar da rikici a cikin al'umma, don haka ya bukaci 'yan sanda su tura jami'ai dauke da makamai a yankin domin dawo da zaman lafiya.
Hotunan auren wani me tura baro sun dauki hankula

Hotunan auren wani me tura baro sun dauki hankula

Uncategorized
Wannan wani me sana'ar turin Baro ne da hotunan sa suka dauki hankula a shafukan sada zumunta.   Matashin da ya fito daga jihar Filato kuma za'a daura aurensa ne a Pankshin dake jihar. Sunansa Joseph Bango sai matar tasa, Hezekiah Gonzuk.   Da yawa sun bayyana sha'awa ganin cewa bai bari sana'ar da yake ga hanashi samun farin ciki ba.
Jihar Filato ma ta baiwa mutane awanni 48 su dawo da abincin da suka wawushe

Jihar Filato ma ta baiwa mutane awanni 48 su dawo da abincin da suka wawushe

Uncategorized
Hukumar 'yansanda a jihar Filato tace ta baiwa mitanen da suka wawushe kayan Abinci a rumbunan ajiya daban-daban nan da ranar Laraba su dawo da su ko kuma su fuskanci kame.   Kakakin 'yansandan jihar, Donbey Peters ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace abinda mutanen suka yi babban laifi ne.   Ya bayyana cewa kwamishinan 'yansanda na jihar yayi Allah wadai da lamarin inda ya bayyanashi a matsayin kokarin lalata aikin da 'yansandan ke yi na kawo tsaro a jihar.   Yace gwamnatin jihar ta baiwa wanda suka wawushe kayan nan da ranar Laraba su dawo dashi ko kuma duk wanda aka kama zai dandana kudarsa.   Yace sun kama sama da mutane 100 game da lamarin.   “He stated that the Government of Plateau State is giving these looters the gra...
Yan bindiga sun kashe shugaban wani kauye tare da wasu uku a sabon harin Filato

Yan bindiga sun kashe shugaban wani kauye tare da wasu uku a sabon harin Filato

Uncategorized
Wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Wereng, da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Filato, ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu ciki har da wani tsohon shugaban riko na kauyen, mai suna Chungyang Mwadkwon. Shaidun gani da ido sun ce 'yan bindigar sanye da kayan tsaro sun mamaye kauyen da daren ranar Litinin, da misalin karfe 9 na dare inda suka harbe wadanda abin ya shafa. Wata ‘yar kauyen, Grace Choji ta ce,“ Da farko, mun yi zaton ‘yan bindigar‘ yan banga ne saboda yadda suka yi ado suka wuce. Amma ba zato ba tsammani, sai suka fara harbi kan duk wanda yake gani, kuma lokacin ne muka san cewa an afkawa kauyen. Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa a Majalisar Wakilai ta Kasa, Istifanus Gyang, ya shaida a Jos ranar Talata cewa an kashe mazauna kauyuka ...
‘Yan Bindiga sun kashe wani Basarake a Jos

‘Yan Bindiga sun kashe wani Basarake a Jos

Siyasa
Wasu 'yan Bindiga sun kashe basarake a Barkin Ladi dake jihar Filato, me suna Bulus Chuwang Jang.   Rahotanni sun bayyana cewa 'yan Bindigar sun kai harinne da daren jiya, Litinin inda suka kashe Magajin garin na Foron. Shugaban matasan Berom a yankin Heipang dake karamar hukumar, Rwang Tengwong ya tabbatarwa da Punch faruwar lamarin.   Hakanan shima kakakin 'yansanda na jihar, Ubah Ogaba ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace tuni an aika da jami'an tsaro yankin.
Yan sanda sun hana malaman firamare yin zanga-zangar lumana a jihar Filato

Yan sanda sun hana malaman firamare yin zanga-zangar lumana a jihar Filato

Uncategorized
Yunkurin da malaman makarantar firamare a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato suka yi na nuna rashin amincewarsu da rashin biyansu albashi, yan sanda sun dakale shi a ranar Laraba. An gano cewa matsalar da malaman ke fuskanta ta fara ne a watan Yulin wannan shekarar lokacin da karamar hukumar ta gaza biyan su albashin watan Yuli tare da sauran ma'aikatan karamar hukumar. Shugaban kungiyar malamai ta Najeriya, reshen Mangu, Isaac Dapul, a lokacin da yake jawabi ga mambobin bayan zanga-zangar lumana da aka shirya, ya ce kokarin da aka yi don ganin shugaban karamar hukumar, Lawrence Danat, ya ga dalilan da za a biya su bashin albashinsu har zuwa watan Agustan wannan shekarar amma hakan ya citura. Dapul ya ce "Tun da shugaban majalisar ba ya shirye ya biya mu hakkokinmu, bai k...