
Hukumar tara haraji ta kasa, FIRS, ta samar da naira tiriliyan N4.178 a cikin watanni 10>>Shugaban Hukumar
Hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) ta ce ta samar da kudaden shiga na tiriliyan N4.178 a cikin watanni 10 da suka gabata.
Shugaban Hukumar, Mista Muhammad Nami ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da rahoto a kan kudaden shigar da aka samu na cikin gida (IGR) a taron 46 na Hukumar Hadin Gwiwar (JTB) da aka yi a Abuja ranar Juma'a.
Nami ya ce abin da aka samu a tsakanin wannan lokacin, ya wakilci kashi 99 na aikin da ya yi na watanni 10 na Naira tiriliyan 4.230.
Ya kuma ce, har zuwa zango na uku na shekarar 2020, tarin kudaden shekara-shekara daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya ya kai Naira biliyan 974.197.
A cewarsa, wannan ya nuna raguwar kashi 1.39 bisa dari idan aka kwatanta shi da tarin daga lokaci guda a shekarar 2019 wanda ya kai N988.024 biliyan.
...