
Cutar Polio: An bai wa Afrika shaidar rabuwa da Polio
Wata hukuma mai zaman kanta dake bayar da shaidar rabuwa da Polio a Afirka ta bayyana cewa nahiyar ta rabu da kwayar cutar ta polio dake watsuwa a cikin al'umma.
Kwayar cutar tana kama yara ne 'yan kasa da shekara biyar, inda a wasu lokutan take nakasa su. A wasu lokutan a kan rasa rai idan har ta kama gabobin numfashi.
Shekara 25 da ta gabata, cutar ta nakasa dubban yara 'yan Afirka.
A yanzu kasashen Afghanistan da Pakistan ne kawai ke fama da cutar a duka fadin duniya.
Polio ba ta da magani, amma riga-kafin da ake digawa yara a baki na ba da kariya.
Najeriya ce kasa ta karshe a nahiyar Afirka da ba a ayyana ta rabu da cutar ta polio mai watsuwa ba, da a turance ake cewa Wild Polio, kasancewar shekara goma da ta gabata...