fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Frank Lampard

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya bukaci kungiyoyi dasu ringa baiwa kocawa lokaci bayan Chelsea ta kori Lampard

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya bukaci kungiyoyi dasu ringa baiwa kocawa lokaci bayan Chelsea ta kori Lampard

Wasanni
Kocin kungiyar Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa ya kamata kungiyoyi su ringa baiwa kocawa lokaci bayan da kungiyar Chelsea ta kori Frank Lampard. Kungiyar Chelsea ta kori Lampard ne bayan daya kwashe watanni 18 yana jagorancin kungiyar, inda Chelsea ta koma ta tara a saman teburin gasar Premier League bayan data fadi wasanni 5 cikin wasanni 8 da suka gabata. Pep Guardiola ya kara da cewa ba wai yana kalubalantar hukuncin da Chelsea ta yanke bane hakan ya dace, amma ya kamata kungiyoyi su ringa baiwa kocawa lokaci a madadin yanke hukunci lokaci guda. Pep Guardiola urges club to give managers time after Chelsea sack Lampard Pep Guardiola says managers need time if they are to succeed – following Frank Lampard's sacking by Chelsea. Lampard was dismissed today afte...
Kungiyar Chelsea tana shirin korar kocinta Frank Lampard

Kungiyar Chelsea tana shirin korar kocinta Frank Lampard

Wasanni
A farkon wannan kakar kungiyar Chelsea tayi kokari sosai yayin da har ake sa ran cewa zata iya lashe kofin Premier League, amma sai dai kungiyar ta koma ta 8 a saman teburin gasar bayan da nasara daya kacal tayi a wasanninta guda shida da suka gabata. Rahotanni da dama sun bayyana cewa mai kungiyar Chelsea, Roman Abraham yana shirin korar Frank Lampard saboda kungiyar Chelsea tana bukatar canji bayan da suka sha kashi daci 3-1 a hannun Manchester City. Kocin Leicester City Bredan Rodgers da tsohon kocin PSG Thomas Tuchel da kuma kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann ne ake sa ran zasu mayewa Chelsea gurbin Lampard wanda ya kashe fiye yuro miliyan 220 wurin siyan sababbin yan wasa a kakar bara.
Manajan Chelsea ya kalubalanci tsarin buga wasannin gasar Premier League

Manajan Chelsea ya kalubalanci tsarin buga wasannin gasar Premier League

Wasanni
Kungiyar Chelsea, wadda ta kasance ta biyar a saman teburin gasar Premier League zata kara da Arsenal ranar sati sannan kuma zata karbi bakunci  Aston Villa ranar litinin, wanda hakan yasa manajan kungiyar Lampard ya kalubalanci tsarin buga wasannin saboda ya banbanta dana sauran kungiyoyi. Tsarin wasannin ya nuna cewa awanni 48 ne tsakanin wasannin Chelsea guda biyu kuma Lampard ya bayyana cewa yan wasa suna cikin hadari idan har suka saki jiki suka jajirce sosai a gabadaya wasannin. A karshe Lampard yace suna bukatar lashe gabadaya makin wasannin kuma akwai wasu kungiyoyin da suke fafatawa a saman teburin gasar wanda su suke da hutun kwanaki uku zuwa hudu tsakanin wasannin nasu kamar su Manchester United,Tottenham da kuma Liverpool.
Frank Lampard ya zamo kocin kasar Ingila na farko daya jagoranci kungiyar Chelsea ta kasance a saman teburin gasar Premier League tun bayan Bobby a shekara ta 1989

Frank Lampard ya zamo kocin kasar Ingila na farko daya jagoranci kungiyar Chelsea ta kasance a saman teburin gasar Premier League tun bayan Bobby a shekara ta 1989

Wasanni
Manajan Chelsea, Frank Lampard ya jagoranci kungiyar ta koma saman teburin gasar Premier League a daren jiya bayan da tayi nasarar lallasa Leeds 3-1 ta hannun Giroud da Zouma da kuma Pulisic. Kuma karo na farko kenan da dan kasar ingila ya jagoranci wata kungiya a gasar Premier League har ta kasance a saman teburin gasar, tun bayan Mike Phelan yayi hakan da kungiyar Hull a watan augusta shekara ta 2016. Yayin da shi kuma Lampard ya zamo kocin kasar ingila na farko daya jagoranci Chelsea ta kasance a saman teburin gasar Premier League tun bayan Bobby Campbell yayi
Ba zan taba tilasawa wani daga yan wasan mu cewa sai sun maye mana gurbin Eden Hazard ba>>Lampard

Ba zan taba tilasawa wani daga yan wasan mu cewa sai sun maye mana gurbin Eden Hazard ba>>Lampard

Wasanni
Manajan Chelsea, Frank Lampard ya bayyana cewa baya danganta Ziyech da Hazard yayin daya bukaci tauraron dan wasan nashi Hakim ya cigaba da kamar yadda yake yi, kuma jajircewar dan wasan ce tasa ake sa ran zai iya mayewa Chelsea gurbin Hazard. Chelsea tasha gwagwarmaya wurin maye gurbin Eden Hazard tunda ya koma kungiyar Real Madrid, amma yanzu har ta kai ga ana danganta Ziyech da Hazard sakamakon nasarar daya yi na cin kwallaye biyu da kuma taimakawa wurin cin kwallaye uku a wasanni biyar. Amma duk da haka shi dai Lampard ya bayyana cewa ba zai danganta Ziyech da Hazard ba inda yake cewa "Abu mai matukar wuya a samu dan wasan da zai iya maye gurbin Hazard saboda shi din na daban ne". "Kuma ni ba zan tana lisatawa wani daga cikin sababbin yan wasan da muka siyo ba cewa dole ...
Akwai kyakkawar alaka tsakanina da Mourinho amma, aikin koci ya fara kawo mana tangarda a lamuran mu>>Lampard

Akwai kyakkawar alaka tsakanina da Mourinho amma, aikin koci ya fara kawo mana tangarda a lamuran mu>>Lampard

Wasanni
Frank Lampard zai kara karawa da Jose Mourinho ranar lahadi yayin da Tottenham zata ziyarci Chelsea, kuma Chelsea tayi nasarar cin gabadaya wasannin data buga da Spurs tunda Lampard ya fara jagorancin kungiyar. Lampard yaji dadin aiki a karkashin jagorncin Mourinho sosai a kungiyar Chelsea, yayin da suka yi nasarar lashe kofuna biyar a shekaru uku wanda suka hada da Premier league guda biyu da FA Cup da sauran su. Lampard ya kawo karshen shekaru 13 daya yi yana wasa a Chelsea shekara 2014, bayan Mourinho ya kara dawowa kungiyar karo na biyu, kuma yanzu zasu kara hadu amma wannan karin fafatawa zasu yi a gasar Premier league. Lampard ya bayyana akwai kyakkwar alaka tsakanin shi da Mourinhk amma aikin kocin daya ke yi da kuma takara a harkar wasan kwallon kafa ta fara kawo masu tang...
Manajan Chelsea Frank Lampard ya zabi gwanin shi tsakanin Messi da Ronaldo

Manajan Chelsea Frank Lampard ya zabi gwanin shi tsakanin Messi da Ronaldo

Wasanni
Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun kasance manyan abokan takara a duniyar wasan kwallon kafa fiye da shekaru goma da suka gabata yayin da kuma suka sunayen su suka shiga cikin jerin zakarun yan wasan kwallon kafa na duniya bakidaya. Lionel Messi ya buga gabaya wasannin shi a kungiyar Barcelona wadda yayi kusan shekaru 20 a kungiyar kuma yayi nasarar cin kwallaye 636 a wasanni 737 daya buga. Messi ya lashe kofunan La Liga sau goma a Barcelona tare da kofunan gasar zakarun nahiyar turai guda hudu. Shi kuma Cristiano Ronaldo ya buga wasannin shine a kungiyar Sporting CP, Manchester United, Real Madrid da kungiyar shi ta yanzu wato Juventus. Cristiano yayi nasarar cin kwallaye 641 a wasanni 852 yayin da kuma ya lashe kofunan mayan gasa na wasan kwallon kafa a kasashe guda uku tare d...
Sheffield 3-0 Chelsea:Sun fi mu karfi>>Lampard

Sheffield 3-0 Chelsea:Sun fi mu karfi>>Lampard

Wasanni
Kwallayen McGoldrick guda biyu da kwallon McBurnie sun taimakawa Sheffield United a jiya yayin da suka ba Chelsea kashi har 3-0, bayan Chelsea sun yi nasara akan Palace da Watford. Manajan Chelsea Frank Lampard ya bayyana cewa wasanni biyu da aka cisu cikin wasanni hudu da suka gabata babban sako ne ga tawagar tashi wanda watakila zasu iya tsintar kansu ana biyar idan har United suka yi nasara a wasan su da Southampton. Bayan an tashi wasan Lampard yace Sheffield United sun fi su a zahirance, sun fi su yin kokari a wasan, kuma sun fisu yin wasa da kwallon. A karshe ma yace sun fisu karfi. Kuma shi maganar Sheffield United kawai yake ji yayin da suke buga wasan. Ya kara da cewa watakila zasu tsinci kansu na biyar a saman teburin gasar amma duk da haka zasu cigaba da kokari domin su...
Chelsea sun samu matsala da kochin su Lampard akan maganar siyan Timo saboda Aubameyang

Chelsea sun samu matsala da kochin su Lampard akan maganar siyan Timo saboda Aubameyang

Wasanni
Kungiyar Chelsea suna harin siyan tauraron dan wasan RB Leipzig Timo Werner wanda aka sawa farashin euros miliyan 53 amma sai dai ba kowa bane ya amince da wannan maganar ba a kungiyar. Babban kochin kungiyar Frank Lampard da mai bada shawara Peter Cech sun bukaci kungiyar da su siya dan wasan Arsenal Pierre Emrick Aubameyang, yayin da Arsenal zasu siyar da dan wasan a farashi mai sauki saboda watanni 12 ne suka rage mai a kungiyar. Chelsea sun yi yunkurin siyan Abameyang a watan janairu amma Arsenal basu amince ba, yanzu kuma sun shirya siyar da dan wasan nasu a karshen wannan kakar wasan. Abameyang ya kasance babban dan wasan da Lampard yake so ya siya a yanzu. Shima Timo yana cikin yan wasan da Lampard yake harin siyan amma ya bayyana cewa ya fi son kwararren dan wasa mai...