
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa ta umarci jami’anta da su koma bakin Aiki
A ranar Juma'ar da ta gabata ne Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC ta umarci dukkan jami'anta da su ci gaba da gudanar da ayyukansu a dukkannin sassan kasar.
Rundunar ta dakatar da duk wasu ayyukan ta a fadin kasar sakamakon rikice-rikicen da suka biyo bayan zanga-zangar adawa da rundunar 'yan sanda ta SARS.
Hukumar ta bukaci Jami'anta da su koma bakin aikin ne ta cikin sanarwar da jami'in rundunar Boboye Oyeyemi ya fitar a ranar juma'a.
A karshe ya jajantawa wadanda hatsarin mota ya rutsa da su a jihar Enugu inda mutane 21 suka rasa rayukansu a ranar Laraba.