Yan bindiga sun kashe jami'an dake lura da ababen hawa akan titi na FRSC guda biyu a karamar hukumar Aguata dake jihar Anambra.
Inda kuma wani mutun ya samu rauni yayin da yan bindigar suka budewa jami'an wuta.
Kuma hukumar ta FRSC ta tabbatar da faruwar wannan lamarin.
Hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC tayi gargadin matuka da su kaucewa shan kwayoyi ko abubuwan dake saka maye a yayin da suke tuki domin kaucewa hadura a lukutan da suke gudanar da bukukuwan ranar Masoya.
Jami'in hulda da Jama'a na hukumar Bisi Kazeem, shine yayi wannan jan kunnan a ranar Lahadi A babban birnin tarayya Abuja.
Hukumar Kiyaye hadura ta kasa reshan jihar Enugu ta aike da sakon gargadi ga Direbobi kan kaucewa gudun ganganci a sabuwar shekarar 2021 da muke ciki.
Kwamandan hukumar Mista Kalu Ogbonnaya shine ya bayyana hakan ga Manema labarai a jihar, inda ya ce mafiya yawan haduran da ke afkuwa a jahar yana da nasaba da gugun ganganci.
Hakanan kwamandan ya gargadi Direbobi da su kaucewa shan muggan kwayoyi a yayin da suke kan tuki inda ya ce hakan na haifar da hadura a kan hanyoyi.
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta bayyana cafke wasu mutum 79 da aka samu da laifin sabawa dokokin hanya tsakanin watan Disamba zuwa 24 ga watan a jihar Akwa Ibom.
Kwamandan sashin hukumar FRSC dake jihar Akwa Ibom, Mista Oga Ochi, shine ya bayyana hakan a wata hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Uyo ranar Lahadi.
Ochi ya ce an kama masu laifin ne saboda laifuffukan da suka hada da yin lodi fiye da kima, tuki da tsofaffin tayoyi, tuki ba tare da lasisin tuki ba, tare da takardun mota na bogi.
A cewarsa, tuni masu laifin da aka kama sun biya tara kamar yadda doka ta tanada.
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta shawarci masu ababen hawa da su yi biyayya ga dokokin hanya domin kauce wa hadurra a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Kwamandar sashin hukumar FRSC dake jihar Ebonyi, Misis Stella Uchegbu, ce ta ba da shawarar a ranar Asabar a lokacin da 'take fadakar da mutane sanin muhimmancin kiyaye dokokin hanya musamman a lokatan karshan shekara.
Uchegbu ta ce watannin karshan shekara lokuta ne da wasu masu ababan hawa ke amfani dashi wajan yin tukin ganganci Wanda hakan ke zama barazana ga rayuwar mutane da su kansu dirobin.
A karshe ta bukaci da masu Ababan hawa su lura tare da yin biyayya da Dokokin hanya Dan kaucewa fadawa cikin Nadama.
Hukumar FRSC ta bayyana cewa 4 daga cikin maaikatanta da masu garkuwa da Mutane suka sace sun kubuta bisa taimakon sauran jami'an tsaro.
Saidai hukumar tace har yanzu akwai sauran jami'anta 6 dake hannun masu garkuwa da mutanen. Hadimin dake kula da ilimantar da jama'a na huku3, ACM Bisi Kazeem ya bayyanawa manema labaran Kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN haka a Abuja.
Jamj'an hukumar 26 ne dake tafiya daga Kebbi zuwa Sokoto dan halartar wani horo na musamman suka gamu da harin 'yan Bindigar inda 2 suka rasu, 10 suka bace, 8 suka tsira ba tare da wani Rauni ba sai kuma 6 suka jikkata.
Shugaban hukumar, Boboye Oyeyemi ne ya nemi sauran jami'an hukumar kada gwiwarsu ta yi sanyi wajan bautawa kasa inda ya nemi da su ci gaba da jajircewa wajan aikinsu.
...
Rundunar ‘yan sanda reshen babban birnin tarayya Abuja, ta yi nasarar cafke wani da ake zargi, Hamisu Tukur, mai shekaru 25, bisa zargin satar motar hukumar kiyaye haddura ta kasa, (FRSC) a Hedikwatar ta da ke Abuja.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda dake babban birinin tarayya Abuja DSP Anjuguri Manzah ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar.
A cewarsa, jami'an 'yan sanda daga ofishin hukumar dake Bwari sune suka cafke wanda ake zargin a ranar Asabar a lokacin da suke kan gudanar da aikin tsaro, bayan da su ka samu kiran waya daga hedkwatar Hukumar kiyaye hadura kan lamarin.
Ya kara da cewa abubuwan da aka samu a hannun wanda ake zargin sun hada da farar Toyota Hilux- mai lamba HQ-26RS da kuma mukulli guda da...
Rundunar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Jigawa (FRSC), ta ce ta tura jami’ai 356 domin tabbatar da tsaron lafiyar masu ababen hawa da sauran masu amfani da titin yayin hutun Eid-el-Kabir a jihar.
Mista Ado Adamu, kakakin hukumar FRSC a jihar, shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a Dutse ranar Alhamis.
Rundunar ta ce, jami'an da aka tura sun hada da ofisoshi 89, da kuma mashals 267 da kuma mashals na musamman 1000.
Kwamandan ya ce an kuma tattara motocin sintiri guda bakwai da motocin daukar marasa lafiya guda uku don yin sintiri na Musamman kwana 10 na Sallah, wanda zai fara a ranar 29 ga Yuli.
Ya yi gargadin cewa: "Hukumar FRSC a shirye take ta kama direbobi da direbobin babura da aka same su da keta ka'idojin zirga-zirgar ababen hawa kafin, lokacin, da ku...