fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: Fulani

Sheikh Gumi ya bayyana dalilin da yasa ‘yan Bindiga ba zasu iya aje makamansu ba

Sheikh Gumi ya bayyana dalilin da yasa ‘yan Bindiga ba zasu iya aje makamansu ba

Uncategorized
Shehin malamin addinin Islama,  Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa idan gwamnati bata baiwa 'yan Bindiga tabbacin tsaron rayuwarsu ba, da wuya su ajiye makamai.   Yace sun shiga daji kuma sun nunawa wadannan Fulani cewa za'a sauraresu, yace kuma Fulanin a shirye suke su ajiye makamansu.   Yace suna da matsaloli irin nasu, baau da ilimi, kuma babu wata kasa da take son zaman lafiya da ci gana da zata bar mutanenta cikin jahilci.   Yace idan dai da gaske gwamnati take ya kamata a yiwa wadannan Fualni Afuwa kamar yanda akawa Tsageran Naija Delta. Ahmad Gumi, an Islamic cleric, says if bandits are not assured of their safety and rehabilitation, they will not let go of their arms. Gumi made the comment on Wednesday during a virtual event hosted by the Nati...
Yan bindiga sun kashe wani shugaban Fulani, Alhaji Maijama’a a Kaduna

Yan bindiga sun kashe wani shugaban Fulani, Alhaji Maijama’a a Kaduna

Tsaro
Gwamnatin jihar Kaduna a yammacin Litinin ta ce wasu ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban al’ummar Fulani a yankin Doka da ke karamar hukumar Kajuru, Alhaji Lawal Musa, wanda aka fi sani da Alhaji Maijama’a. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishina Samuel Aruwan, Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Kaduna ya fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce: “Jami’an tsaro ne suka sanar da wannan ga Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Lahadi. Alhaji Lawal Musa ya kasance shugaban al’ummar Fulani a yankin Doka da ke karamar hukumar Kajuru wanda ya yi aiki kafada da kafada da sauran shugabannin al’ummar wajen cimma nasarar kokarin samar da zaman lafiya a yankin. “Wasu‘ yan fashi da makami sun kashe Alhaji Lawal Musa a gidansa, a gaban danginsa. “Yana ...
Bai kamata yanda Duniya ta ci gababa ace har yanzu ana yawo da Shanu guri-guri da sunan kiwo ba>>Adamu Garba

Bai kamata yanda Duniya ta ci gababa ace har yanzu ana yawo da Shanu guri-guri da sunan kiwo ba>>Adamu Garba

Uncategorized
Dan jam'iyyar APC kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Adamu Garba ya bayyana cewa bai kamata a ce a shekarar 2021 ba, yanda Duniya ta ci gaba ba, ace har yanzu ana jawo da shanu daga guri zuwa guri da sunan Kiwo.   Adamu ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta a yayin da cece-kuce ke ci gaba da gudana akan korar da wasu jihohin yarbawa ke son yiwa fulani makiyaya da kuma zargin Fulanin bisa aikata laifukan ashsha.   Yace ya kamata Gwamnati da Fulani masu kudi su tashi tsaye wajan samar da rugage da wajan kiwo na zamani ga Fulanin.   Yace kuma ya kamata a wayar da kan Fulanin su san cewa kowane Fili akwai meshi, kuma ana mallakarsa ne kawai ta hanyar ko dai haya ko kuma saye.   Yace ya kamata a jawo Fulanin a jiki kuma a riga ...
Akwai yiyuwar daukar matakin ramuwar gayya a Arewa kan harin da aka kaiwa Fulani a Kudu>>ACF

Akwai yiyuwar daukar matakin ramuwar gayya a Arewa kan harin da aka kaiwa Fulani a Kudu>>ACF

Tsaro
Kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF ta bayyana cewa akwai yiyuwar daukar matakin ramuwar gayya a Arewa kan harin da aka kaiwa Fulani a kudu.   Sakataren yada labaran ACF, Emmanuel Yawe ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda yace mafi ban takaici kan harin shine yanda an sanar da jami'an tsaro kamin faruwarsa sannan kuma Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro suna kallo aka kaiwa Fulanin hari.   Yace suna kira ga hukumomin jiha dana Taraya su tabbatar an dauki mataki akan lamarin saboda da irin wadannan hare-haren dana ramuwar gayya ne yakin basasa ya fara a shekarun baya.   Kungiyar tace dolene a dauki matakin kama wanda suka kai wadannan hare-haren a kuma hukuntasu ida kuma hakan bata faru ba to lallai akwai yiyuwar kai hare-haren ramuwar ...
Hotuna yanda Matasa suka Kona gidan Sarkin Fulani a Oyo jami’an tsaro suna Kallo

Hotuna yanda Matasa suka Kona gidan Sarkin Fulani a Oyo jami’an tsaro suna Kallo

Uncategorized
Matasan Yarbawa sun farwa gidam Sarkin Fulani a jihar Oyo inda suka konashi suka kuma fitar dashi daga gidan.   Akwai Rahoton dake cewa ma sun kashe matar sarkin Fulanin, kamar yanda BBChausa ta ruwaito.   Saidai Sahara Reporters ta bayyana cewa, Sarkin Fulanin, Alhaji Saliu Abdulkadir ya bayyana mata cewa an kona gidan nasa da Motoci kuma an jikkata 'ya'yansa.   Hakanan a kona wasu karin gidaje 11 na Fulani a jihar. Ya bayyana cewa duk da tabbacin tsaro da jami'an tsaron suka basu, amma a gabansu ne aka kona masa gida. "As we speak, we are in the bush. Our cars, numbering about 11, have been burnt. Some of my children sustained injuries and we are looking for a way to get them to hospital. My children have left their houses for the bush. We need ...
Duk bafulatanin da ya shigo mana jiha da sunan dan banga zamu daureshi>>Gwamnan Benue

Duk bafulatanin da ya shigo mana jiha da sunan dan banga zamu daureshi>>Gwamnan Benue

Uncategorized
Gwamnan Jihar Benue,  Samuel Ortom ya gargadi fulani da cewa ba zai yadda da kungiyar 'tan Banga da tace zata kafa ta shigar masa jiha ba.   Gwamnan ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, inda yace suna da 'yan bangarsu da kuma 'yansandan jiha da yanzu suke tsara ayyuksnsu dan haka ba zasu yadda Fulanin su shigo musu da sunan yan banda ba. Kugiyar Miyetti Allah ta fulani a baya ta bayyana cewa zata kafa kungiyar 'yan banga 'yan Fulani da zata rika kare Fulanin a fadin Najeriya. Hutudole ya fahinci cewa kungiyar ta yi barazanar kai Gwamna Ortom kotu idan bai janye wadannan kalaman nasa ba.   Saidai gwamnan ya jaddada cewa ba zai bari kungiyar ta shigar masa jiha da sunan 'yan Banga a wa mutanenshi aika-aika ba.
Fulanine kashin bayan rashin ci gaban Najeriya>>Kungiyar kare murdin Inyamurai

Fulanine kashin bayan rashin ci gaban Najeriya>>Kungiyar kare murdin Inyamurai

Siyasa
Kungiyar matasan kabilar Inyamurai ta OYC ta bayyana cewa babbar matsalar koma baya a Najeriya, Kabilar Filani ce.   Shugaban kungiyar, Igboayaka O. Igboayaka ne ya bayyana haka inda yace a cikin shekaru 50 da Najeriya ta shafe da 'yancin kai, an samu shuwagabannin kasashe na soja 5 da kuma na dimokradiyya 3 da Fulanine amma Kasar ta kasa ci gaba. Yana wannan maganane a matsayin martani ga Rahoton dake cewa Shugaban kungiyar matasan Arewa yace Inyamuri ba zai mulki Najeriya ba.   Yayi kira ga 'yan Arewar da kudu da su dage wajan ganin sun zai Inyamuri dan shine zai iya kawowa kasarnan ci gaban da ake bukata.
Majalisa ta goyi bayan gwamna Ganduje inda ta bukaci a hana Fulani daga kasashen waje shigowa Najeriya

Majalisa ta goyi bayan gwamna Ganduje inda ta bukaci a hana Fulani daga kasashen waje shigowa Najeriya

Uncategorized
Majalisar wakilai a zaman da ta yi a yau,Talata ta bukaci gwamnatin tarayya data hana Fulani Makiyaya shigowa kasarnan daga kasashen waje.   Dan majalisar, Ndudi Elumelu ne ya fara taso da batun inda yace Fulanin dake shigowa Najeriya daga kasashen waje ne ke rike bindiga kuma suna kashe mutane, harma jami'an tsaro da dama sun shaida haka. Ya kara da cewa matsalar irin wannan fulani kusan daya take data Boko Haram amma an fi baiwa Boko Haram Muhimmancin.   Da yake magana akan wannan kuduri, kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya baiwa kwamitocin Majalisar kan Sojoji da 'yansanda dasu zauna da jami'an tsaron kasarnan dan fito da mafita akan wannan matsala.
Shugaban karamar Hukuma a jihar Delta ya baiwa Fulani kwana 7 su tashi daga mazaunansu

Shugaban karamar Hukuma a jihar Delta ya baiwa Fulani kwana 7 su tashi daga mazaunansu

Tsaro
Shugaban karamar hukumar Oshimili North dake jihar Delta, Louis Ndukwe ya baiwa Hausa Fulani dake zaune a dazukan yankin kwanaki 7 da su fice daga gurin ko kuma su hadu da fushin hukuma.   Wannan daliline yasa Fulanin dake suka fito suna zanga-zangar nuna adawa da wannan mataki. Da yawansu sunce sun zama 'yan jihar Delta dan idan aka koresu daga nan, basu san inda zasu koma ba dan a nan aka haifesu iyaye da kakanni.   Da yake magana a madadin Fulanin, Me magana da yawun Kungiyar Lauyoyi Musulmai na jihar, Idris Abubakar ya bayyana cewa wannan umarni bai kamata ba.   Yace ya tabbata gwamnan jihar bai san da wannan Umarni ba kuma suna Allah wadai dashi. Yace maganar sata da kisa ya kamata 'yansanda su tsananta bincike dan ta iya yiyuwa 'yan cikin garin...

Kada ku kara shigowa jihohinmu da shanu a kafa>>Gwamnonin Inyamurai suka gayawa Fulani

Uncategorized
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kungiyar gwamnonin yankin Inyamurai sun cimma matsaya da fulani makiyaya da kada su sake zuwar musu da shanu ta kafa watau irin yanda sukan tafiya dasu dinnan suna kiwo zuwa jihohinsu saidai ta kan titi a cikin motoci. Wannan na cikin sanarwar da Farfesa simon Ortuanya ya fitar ya fitar kamar yanda yake a cikin rahoton jaridar Punch na labarin yau. Yace akwai fulani makiyaya da suke a yankin kuma ana zaune dasu lafiya, kai wasu ma a nan aka haifesu amma daga baya sai aka fara samun satar mutane dan kudin fansa da kuma rashin jituwa dake kai ga fadace-fadace. Wannan yasa suka zauna da fulanin dake yankin suka kuma cimma matsayar cewa fulanin ne ke aikata irin wadancan aika-aika amma irin wanda ke shiga yankunan ta kafa ta ...