
Fulham 2-3 Everton: yayin da Calvert Lewin ya taimakawa Everton da kwallaye biyu ita kuma Fulham ta cigaba da barar da penariti
Tauraron dan wasan Everton Richarlison ya cigaba da jajircewa bayan daya kammala dakatar da shi daga wasanni uku da aka yi, yayin daya taimakawa Calvert Lewin yayi nasarar ciwa Everton kwallo guda cikin minti daya da fara wasan nasu.
Decordova ya ramawa Fulham kwallon da Lewin ya zira masu a minti na 15 yayin da shi kuma dan wasan Ingilan Calvert ya kara zira wata kwallon da taimakon Digne wadda tasa ya kasance dan wasan daya fi zira kwallaye a gasar Premier League wannan na kakar da kwallaye 10.
Dan wasan baya na faransa Digne ya kara taimakawa Doucoure ya ciwa Everton kwallon ta uku a wasan wadda tasa kungiyar ta lashe gabadaya maki uku na wasan duk da cewa Fulham ta kara zira kwallo guda ta hannun Lucas Loftus.
Sakamakon wasa yasa yanzu Fulham ta fadi wasanni bakwai...