
Mafi yawan munanan laifukan da ake aikatawa a jihar Borno, Fyadene>>Ndume
Mai shari'a,A'isha Ndume ta bayyana cewa, kaso 90 cikin 100 na laifukan da ake aikatawa a jihar Borno Fyadene.
Ta bayyana hakane a wajan wani taron bita da aka yi a kan 'yancin mata da kuma tuntuba tsakanin masu ruwa da tsaki a bangaren Shari'a.
Taron an yi shine bisa hadin gwiwar kasar Netherland da Majalisar Dinkin Duniya, UN.