fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Gana

Sojojin Najeriya sun yi artabu da yaran Gana inda suka kashe 2 da kama 5

Sojojin Najeriya sun yi artabu da yaran Gana inda suka kashe 2 da kama 5

Tsaro
Sojojin Najeriya dake rundunar Operation Whirl Stroke dake yaki da ayyukan ta'addanci a yankin Arewa ta tsakiya sun farwa wata maboyar yaran Marigayi, Terwase Agwaza,  wanda aka fi sani da Gana.   Sojojin sun kaiwa Maboyar 'yan Bindigar hari ne bayan samun bayanan Sirri inda kuma suka kashe 2 daga ciki tare da kama 5. Kakakin hedikwatar tsaro ta kasa, Janar John Enenche ne ya bayyana haka ga manema labarai yace harin ya farune a Adu dake Chanchangi jihar Taraba.   Hakanan sojojin sun kuma kai hari a Katsina Ala dake jihar Benue inda suka kama wasu masu laifi da kwayoyi da makamai da sauransu. Yacw wanda ake zargin na fuskantar bincike inda daga baya za'a mikasu hannun 'yansanda.
Yanda Gana ya binne ‘yar Cikinsa me shekaru 12 da ranta dan yin tsafi

Yanda Gana ya binne ‘yar Cikinsa me shekaru 12 da ranta dan yin tsafi

Uncategorized
Bayanai dai na ci gaba da fitowa game da dan ta'addan jihar Benue da Sojoji suka kashe, watau Terwase Agwaza wanda aka fi sani da Gana.   Wani daga cikin yaran Gana da TheNation ta yi hira dashi, Aondehemba wanda ake kira da Major ya bayyana cewa me gidan nasu nada Sihiri sosai. Yace dalilin ma da yasa sojoji suka kasa kamashi kenan a duk sanda suka je kamashi sai kawai ya bace, yace ko ranar da Sojoji suka kama Gana yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Makurdi dan amsar Afuwar gwamnati, Tsafin baya tare dashine, ya baiwa wani yaronsa saboda shi ya tuba.   Yace Gana ya samu wannan tsafinne ta hanyar binne diyarsa me shekaru 12 da ranta.
Gana nada yara 200 a daji da basu tubaba>>Wani yaronsa ya fada

Gana nada yara 200 a daji da basu tubaba>>Wani yaronsa ya fada

Uncategorized
Wani yaron gawurtaccen dan ta'addarnan na jihar Benue, Marigayi, Terwase Agwaza wanda aka fi sani da Gana da sojoji suka kashe ya bayyana cewa Gana nada yara 200 a daji da basu tubaba.   Wanda ake kira da Aondehemba da aka fi sani da Major ya bayyana cewa, Gana na da mayaka 200 da yawa horo kuma suna cikin dazukan Taraba da Benue. Yace baban dalilin da yasa aka kama gana bai bace ba shine sabosa ya rika ya baiwa mataimakinsa duk wani Sihiri da yake dashi saboda dama yayi tsammanin za'a kashe shi a wajan wanan sulhun. Major yace suna tare da su Gana sojoji suka je daukar Ganan amma shi sai ya bace yace amma Gana bai bace ba saboda ya baiwa mataimakinsa duk wani tsafi dake gareshi yace idan an kasheshi ya jagoranci kungiyar a ci gaba da abinda ya bari.   Yace Gan...
Idan aka kasheni yayin Sulhu ku daukar in fansa>>Gana ya gayawa Yaransa kamin ya mika wuya

Idan aka kasheni yayin Sulhu ku daukar in fansa>>Gana ya gayawa Yaransa kamin ya mika wuya

Tsaro
A ranar 8 ga watan Satumba ne karshen gawurtaccen dan ta'adda da ake nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza,  Wanda aka fi sani da Gana tazo karshe.   Sojoji ne ake zargi da kamashi a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Makurdi dan karbar afuwar Gwamnati inda suka tafi dashi suka kasheshi, saidai sojojin sun ce a musayar wuta suka kashe Gana.   Dan Bindigar yayi Rayuwa da ikirarin cewa yana kare al'ummarsa ta Tibi ne amma ana zarginsa da kashe mutane ba gaira ba sabab da garkuwa da mutane da kuma dorawa mutane harajin dole.   An kuma zargi Gana da binne mutane da ransu sannan an zargeshi da kashe sarakuna da dama a yankin da yake ta'asarsa.   Saidai Rahotanni da Vanguard ta samo sun bayyana kamin Gana ya fito daga inda yake boye dan mika wuya, ya barwa...
A biyamu ladar Miliyan 50 da aka saka akan Gana saboda mun kasheshi>>Sojoji suka nema

A biyamu ladar Miliyan 50 da aka saka akan Gana saboda mun kasheshi>>Sojoji suka nema

Uncategorized
Rahotanni na nuna cewa sojojin Najeriya na neman a biyasu ladar Miliyan 50 da aka saka akan gano dan ta'addar jihar Benue, Terwase Agwaza,  watau Gana.   Sojojin sun kashe Gana wanda suka ce a musayar wuta ya mutu. Saidai gwamnan Benue, Samuel Ortom ya bayyana shakku akan wannan ikirari saboda Gana ya riga ya ajiye makamai yana neman Afuwa. Wata majiya daga gidan Sojan ta gayawa TheNation cewa sojojin na jira su ga Gwamnati  jihar Benue zata cika alkawarin data dauka na biyan kudin lada akan Gana da suka kashe.   Yace Gwamnatin jihar Benue ta saka ladar Miliyan 10 akan Gana, jim kadan bayan da aka kasa ganoshi kuma ta kara kudin ladar zuwa Miliyan 50. Yace bawai kudin ne sojojin ke kwada yi ba amma suna son ganin idan gwamnati zata cika Alkawarin data dauka.
Matar Gana ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya ta diyyar Biliyan 5 na kashe mata miji

Matar Gana ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya ta diyyar Biliyan 5 na kashe mata miji

Uncategorized
Matar gawurtaccen dan ta'adda da sojoji suka kashe a jihar Benue, Wator Akwaza ta bayyana cewa mijinta ya shirya barin rayuwar da yake dan komawa ga Allah yayin da sojoji suka kasheshi.   Matar tace da farko da aka kaiwa Gana maganar Afuwa yace be yadda ba sai idan an saka Sanata Gabriel Suswan a ciki. Tace Suswan ya sameshi inda ya bashi tabbacin cewa babu abinda za'a masa. Ya fito ya mika makamansa wajen gwamnati kwatsam suna tafiya zuwa Makurdi sai ta ji labarin an kasheshi. Tace tana kira ga gwamnati data binciki lamarin sannan kuma a biyata diyyar Biliyan 5.
Bidiyon Gawurtaccen dan ta’addan Benue, Gana na bayanin yanda aka bashi Miliyan Dari uku da yanda zai baiwa jami’an tsaro cin hanci kamin sojoji su kasheshi

Bidiyon Gawurtaccen dan ta’addan Benue, Gana na bayanin yanda aka bashi Miliyan Dari uku da yanda zai baiwa jami’an tsaro cin hanci kamin sojoji su kasheshi

Uncategorized
Kisan da Sojojin Najeriya sukawa Terwase Agwaza wanda aka fi sani da Gana, Gawurtaccen dan ta'addan wanda ake nema ruwa a jallo bayan da ya ce ta tuba ya jawo cece-kuce.   Gwamnan jihar Benue,  Samuel Ortom ya bayyana Kaduwa da kisan da sojojin suka masa inda yace a masa bayanin yanda abin ya faru. An zargi sojojin da kwace Gana daga tawagar da ta tafi kaishi gidan gwamnati dan a masa afuwa inda daga baya suka ce sun kasheshine a musayar wuta.   Wannan dalili yasa akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi,  a wata hira da Channelstv ta taba yi dashi, Gana yayi ikirarin cewa Fulani sun bashi kwangilar mamaye jihar Taraba inda shi kuma ya nemi su bashi Biliyan 1, saidai a karshe sun ce zasu bashi Miliyan 350 amma yace sun yi kadan saboda suma jami'an tsaron sai ya sammusu wan...
Irin haka fa kisan shugaban Boko Haram ya jawo tada kayar bayan kungiyar>>Tsohon Gwamnan Benue, Suswan yayi Allah wadai da kisan Gana

Irin haka fa kisan shugaban Boko Haram ya jawo tada kayar bayan kungiyar>>Tsohon Gwamnan Benue, Suswan yayi Allah wadai da kisan Gana

Tsaro
Tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswan yayi Allah wadai da kisan da sojoji sukawa Dan ta'adda, Terwase Agwaza wanda aka fi sani da Gana bayan da ake tsammanin ya tuba.   Suswan ya bayyana cewa tashe-tashen hankula a mazabarsa ta Benue ne ya sanya shuwagabannin al'umma na yankin suka yanke shawarar zama dan yawo hankalin 'yan ta'adda su ajiye makamansu kuma suka amsa kira. Yace Abin Farin ciki shine Gana da yaransa sun ajiye makamai amma yayin da suke kan hanyar zuwa wajan gwamnan jihar dan ganawa dashi sai sojoji suka tare tawagar motoci suka tafi dashi. Yace daga baya sai ga gawarsa an aje masa wata Bindiga a kusa dashi da ikirarin cewa wai an yi musayar wuta dashi.   Yace wanda suke tare dashi da sojojin suka kwaceshi sun ga cewa babu wani makami a...
Na kadu da kisan Gana, Sai sojoji sun min bayanin yanda aka yi>>Gwamnan Benue

Na kadu da kisan Gana, Sai sojoji sun min bayanin yanda aka yi>>Gwamnan Benue

Tsaro, Uncategorized
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa ya kadu da kisan gawurtaccen dan ta'adda da ake nema ruwa a jallo da Sojoji suka yi.   A jiyane dai Gana ya mika wuya inda yace ya tuba, saidai yana kan hanyarsa ta zuwa Benue, sai sojoji suka tare motar da yake ciki suka daukeshi shi da wasu tubabbun 'yan ta'addar. Daga baya dai an ga gawarsa inda sojojin suka yi ikirarin cewa sun kasheshi ne a musayar wuta,a cewar gwamna Ortom.   Saidai gwamnan ya bayyana cewa ya kadu da abinda ya faru amma yana neman sojojin su masa bayanin yanda lamarin yake.