
Jihar Kebbi ta sanya hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane
Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya sanya hukuncin kisa kan duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane dan kudin fansa a jihar.
Kwamishiniyar shari'a ta jihar, Hajiya Ramatu Ramatu Adamu Gulma ta bayyana haka a sanarwar data fitar.
NTA ta ruwaito ta tana cewa, wanda kuma aka samu da Fyade hukuncin daurin rai da raine.