fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: garzali miko

Garzali Miko yayi kaura daga Kano

Garzali Miko yayi kaura daga Kano

Nishaɗi
  Fitaccen jarumi kuma Mawaki Garzali Miko, ya koma garin Azare na jihar Bauchi domin cigaba da gudanar da ayyukansa na fina-finai da waka.   Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunan ta, shaidawa Freedom Radio cewa jarumin ya kai akalla wata guda da kwashe kayan sa daga garin Kano, inda ya koma garin Azare da zama.   Ana zargin dai Garzali Miko ya kauracewa Kano ne saboda tsoron sanya ido daga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.   Miko dai na daya daga cikin jaruman da tauraruwar sa ke haskawa a wannan karnin.   Har ila yau, a ranar Asabar din da ta gabata ne, Garzali ya bude wani sabon gidan wasa a can garin na Azare, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.