
Dan shekaru 11 ya mutu a wajan gasar Shan Giya bayan da ya sha kwalba 5
Lamarin ya farune a kasar Malawi, inda yaron dake aji 7 na makarantar Firamare dan shekaru 11, Humphrey Chipeta ya shiga gasar.
Ya kai zagaye na karshe na gasar inda ya kwankwadi giya kwalba 5 kuma daga nan sai ya mutu.
Saidai wani shaida, Emmanuel Chirwa ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya a mutuwar yaron dan kuwa shine ma ya lashe gasar da aka yi ta baya. Ana saka Dubu 20 kudin kasar Malawin ga duk wanda ya lashe gasar.
Lamarin ya farine a yankin Mzimba na kasar inda kuma tuni kungiyoyin kare hakkin yara suka ce zasu shiga maganar, Musamman lura da cewa ba Humphrey ne kadai yaro a cikin gasar ba.