
A daidai wannan lokaci ana bikin rufe Musabakar Alkurani ta kasa da ke gudana a jamiar Bayero ta Kano
Daga Ibrahim Hamisu Kano
Mai alfarma sarkin Musulmi ya iso tare mai martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero tare da manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan.
Yayinda ake dakon sakamakon Musabakar, adai-dai wannan lokaci Limamim masallacin Abuja ne Farfesa Shehu Ahmad Galadanchi ya ke jawabinsa.
A jawabin nasa dai ya maida hankali ne a kan tarihin karantar da karatun A'lkur'ani a Nigeriya da Muhimmancin karanta shi.
A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka fara gasar ta karatun Al-Kur"ani