fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Gasar Rawa

Bidiyo: Suma Kishiyoyi sun shiga gasar yiwa mazajensu rawa

Bidiyo: Suma Kishiyoyi sun shiga gasar yiwa mazajensu rawa

Nishaɗi
Gasar rawarnan da ma'aurata kewa junan su da wakar Hamisu Breaker ta Jarumar mata wadda akewa lakabi da #HusbandDanceChallenge na ci gaba da daujar hankula sosai.   A yayin da wasu ke caccakar masu yin hakan wasu kuwa na yabawa. A baya dai an saba ganin masu mata daya ne ke shiga wnanan sha'ani amma a yanzu masu mata 2 ma sun bi sahu. Bidiyon dake kasa na wasu masu mata 2 ne da suka shiga wannan gasa suma aka yi dasu.  
Gasar Rawar mauratan Arewa: Tau fa, Kilu ta ja Bau: Miji ya Saki matarsa saboda saka hoton rawar data masa daga shi sai ita a Yanar gizo

Gasar Rawar mauratan Arewa: Tau fa, Kilu ta ja Bau: Miji ya Saki matarsa saboda saka hoton rawar data masa daga shi sai ita a Yanar gizo

Auratayya
A yayin da ake ta gasar rawa tsakanin ma'auratan Arewa inda zaka ga mata da miji na rawa tare ko kuma matar nawa mijinta rawa a kuma saka a shafin yanar gizo,Abin ya zama yayi. Saidai ga wani magidanci da yake tare da matarshi shekaru 19 da yara 3, bai ji dadin ganin bidiyon rawar matar tashi a yanar gizo ba.   Hakane tasa ya sake ta duk da cewa ita kadaice matarsa, kamar yanda wani ma'abocin shafin Facebook, Sanusi Bature ya bayyana wanda yace mutumin da yayi sakin, tsohon me gidansa ne. Wasu dai sun yaba da wannan gasa yayin da wasu kuwa da dama suka yi Allah wadai da ita.