
Shugaba Buhari ya jinjinawa dan Najeriyar da ya tsinci kudi a Kasar Japan ya mayar kuma aka bashi lada yaki karba
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jinjinawa dan Najeriya Nkenna Nweke dake kasar Japan da zama wanda kuma dalibin jami'a ne me karatun digiri na 3 sannan kuma yana aiki da jami'ar.
Ya tsinci jakar kudi ne inda ha mayarwa da 'yansanda ita kuma aka bashi kaso 10 cikin 100 na kudin amma yace ba zai kar ba ba.
Dansandan yace masa a dokar kasar Japan idan kaga kudi ka mayar dasu to za'a baka kaso 10 cikin 100 na kudin, saidai Nweke ya bayyana cewa shi Kirista na garine kuma ba haka iyayenshi suka koya masa ba dan haka ba zai karbi kudin ba.
Bayan komawa gida ya bayyana cewa ya samu sako daga hukumar 'yansanda suna jinjina masa akan abinda yayi sannan kuma ya samu sako daga me kudin shima yana mai godiya.
Shugaba Buhari a Ranar Asabar ta bakin me ma...