fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Gawon

Kungiyar Gwamanonin Arewa ta aike da sakon Murnar cikar Tsohon Shugaban Najeriya Gawon shekaru 86

Kungiyar Gwamanonin Arewa ta aike da sakon Murnar cikar Tsohon Shugaban Najeriya Gawon shekaru 86

Uncategorized
An bayyana tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Yakubu Gawon a matsayin jajirtacce kuma dan kishin kasa, wanda yayi aiki tukuri domin cigaban hadin kan kasa. Yayin da yake taya shi murna a yayin bikin cikarsa shekaru 86, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa (NGF) tare da gwamnan jihar Filato, Mista Simon Bako Lalong ya ce Janar Gowon ya kasance daya daga cikin nagartattun shugabannin kasar nan wadanda ke nuna halaye masu kyau na tawali'u da sadaukarwa domin gina kasa da samar da zaman lafiya a kasa baki daya. Hakanan Lalong ya bukace shi da kada ya yi kasa a gwiwa wajen yin amfani da kwarewarsa da iliminsa wajen neman hadin kai da hada kan kasa duk da kalubalen da kasar ke fuskanta.
Sarkin Kano Aminu Ado ya ziyaraci Janar Gawon

Sarkin Kano Aminu Ado ya ziyaraci Janar Gawon

Siyasa
A ranar Litinin din da ta gabata ne Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya kai wa tsohon Shugaban kasa, Yakubu Gowon ziyara. Rahotanni sun bayyana cewa, ziyarar wanda sarkin Kano ya kai wa Tsohon shugaban kasar a gidan sa da ke Abuja ta dauki tsawan mintoci 30. Sarkin Kano na kai ziyarar rangadi ne ga sarakuna, gwamnonin jihohi, manyan ma’aikatan gwamnati da sauran manyan kasa. Sa'annan Ana sa ran Sarkin zai hadu da tsoffin shugabannin Najeriya Ibrahim Babangida da Abdulsalam Abubakar yayin ziyarar kwana biyu da zai kai Minna da Bida a jihar Neja.