
Gowon ya karyata ikirarin Majalisar Dokokin Burtaniya cewa ya ‘saci rabin kudin Babban Bankin Najeriya zuwa Ingila
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Yakubu Gowon, ya musanta zargin da ake yi masa cewa ya kai “rabin kudaden Babban Bankin Najeriya kasar ingila”.
Wani dan majalisar dokokin Burtaniya, Tom Tugendhat, ne ya yi wannan ikirarin yayin muhawara kan harbe-harbe da akayi Lekki ga masu zanga-zanga.
Tugendhat ya ce "mun san cewa a yau, ko da a yanzu, a cikin wannan babban birni namu, akwai, abin bakin ciki, wasu mutane da suka karɓa daga mutanen Najeriya suka ɓoye ribar da suka samu a nan." Ya ce Gowon yana daya daga cikinsu. A cewarsa, Gowon ya dauki rabin CBN zuwa Ingila.
Sai dai kuma, a wata hira da BBC, Gowon ya bayyana zargin a matsayin "karya".
Ya ce: “Abin da dan majalisar ya fada karya ne. Ban san daga ina ya samo wannan shara ba. Na yi wa Najeriya aiki tukuru kuma bayanan ...