fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: General BMB

Ali Nuhu da Adam A. Zango sun aikewa da General BMB kudi bayan gini ya fada masa a kafa

Ali Nuhu da Adam A. Zango sun aikewa da General BMB kudi bayan gini ya fada masa a kafa

Nishaɗi
A baya ne muka ji yanda gini ya fadawa tauraron fina-finan Hausa,  Bello Muhammad Bello a kafa inda har aka masa gyara.   Bellon ya godewa duka wanda suka tayashi jaje na 'yan uwa da abokan arziki. Daga cikin wanda yawa Godiya akwai Sani Musa Danja, Ado Gwanja, Afakallahu da Sauransu.   Bello ya kuma godewa Ali Nuhu inda yace yana godiya bisa kiransa da yayi da kuma kudin da ya aika masa. https://www.instagram.com/p/CGIDzXwJLzJ/?igshid=1os57ha3su3fd   Hakanan Bello Ya kuma godewa Adam A. Zango inda shima yace yana godiya da nuna damuwa da halin da ya shiga sannan kuma da kudin da ya aika masa.   Ya bayyana cewa shi dan APC ne, Adam A. Zango kuma dan PDP amma hakan bai hanasu zumunci ba. https://www.instagram.com/p/CGIFPbJJbb5/?igshid=1kx1cr...
Na fadi Abubuwa marasa dadi a kanka amma ka mayar da komai ba komai ba kana saka min da Alkhairi, wannan irin halin da Annabi(SAW) ya koyarne>>General BMB ga Ali Nuhu

Na fadi Abubuwa marasa dadi a kanka amma ka mayar da komai ba komai ba kana saka min da Alkhairi, wannan irin halin da Annabi(SAW) ya koyarne>>General BMB ga Ali Nuhu

Nishaɗi
Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello wanda aka fi sani da General BMB ya yabi abokin aikinsa, Ali Nuhu inda ya bayyanashi da cewa mutumin kirki ne.   BMB ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumuntar Instagram inda yace Ali Nuhun a koda yaushe ana masa Sharri yana sakawa da Alheri, irin halin da Annabi Muhammad (SAW)   Yace ya fadi abubuwa marasa dadi da dama akan Ali Nuhun amma a koda yaushe yana kokarin ganin ya taimaka masa.   Ali Nuhun ya amsa masa da cewa, Ina Godiya, Allah ya yafe mana Kura-kuren mu. https://www.instagram.com/p/CFdMYxiJKJ1/?igshid=1ihcl7euqs3th
General BMB ya kaiwa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara

General BMB ya kaiwa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara

Nishaɗi, Uncategorized
Tauraron mawakin Hausa, Bello Muhammad Bello wanda aka fi sani da General BMB ya kaiwa shehin Malamin addinin Islama,  Sheikh Dahiru Usman Bauchi ziyara.   A sakon da ya saka a shafinsa na sada zumunta, BMB ya bayyana cewa ya kai ziyara gidan malam kuma an karbeshi hannu biyu-biyu inda ma har aka masa addu'a. https://www.instagram.com/p/CFFl-zgpUz9/?igshid=11qj45u979glf