
Za’a kori ma’aikatan Ofishin jakadancin Najeriya daga Ofishinsu dake Hungary saboda rashin biyan kudin haya
Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa, Osifishin jakadancin Najeriya na kasar Hungary ya aika masa da cewa za'a koresu daga ofishinsu saboda kudin hayar da ake binsu da basu biyaba.
Ya bayyana hakane a yayin da yake kare kasafin kudin ma'aikatar tasa a gaban majalisa a jiya, Talata.
Yace suna samun irin wannan korafe-korafe daga Ofisoshin jakadanci da dama. Yace sannan akwai kudin Alawus din kaya da zasu turawa ma'aikatan Ofisoshin jakadancin duk shekara na Dala 2,500, wanda yace wajan Biliyan 1.2 ne amma yanzu Biliyan 762 garesu a kasa.
Yace akwai Ofisoshin jakadancin Najeriyar da basu da kyan gani sannan wasu ana binsu bashi wanda hakan abin kunya ne ga kasar. Yace dsn hakane suke tunanin kulle wasu daga cikin Ofisoshin Jaladan...