
Idan ba a kula ba, Rikicin da zai faru a Najeriya sai yafi na kasar Somalia Muni>>Ministan Buhari
Ministan kula da ayyuka na musamman na shugaban kasa, Muhammadu Buhari, George Akume yayi gargadin a kula da yanda Najeriya take idan ba haka ba lamari zqi kazanta.
Akume ya bayyana hakane a lokacin nada sabon sakataren ayyukan ibadar Kiristoci, jiya Alhamis.
Akume yace dolene a kula da iyakokin kasarnan da kuna kula da hadin kan 'yan kasa wanda idan ba haka rikicin da zai faru a Najeriya sai yafi na kasar Somalia.
Ya kara da cewa tabbas shugaban kasa, Muhammadu Buhari na iya bakin kokarinsa amma fa har yanzu akwai tarin matsaloli.