
“Na tsiniwa Bukayo Saka sai yasa ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan karshe na gasar Euro”>> Chiellini
Tauraron dan wasan Italiya Georgio Chiellini ya bayyana cewa ya tsinewa Bukayo Saka kafin dan wasan mai karancin shekaru ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan karshe na gasar Euro.
Saka ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron ragar ne sakamakom da Gianluigi Donnarumma daya cire kwallon, wanda hakan yasa Italiya ta doke Ingila ta lashe kofin gasar Euro bayan sun tashi wasa daci 1-1 a mintina 120 da suka buga.
Kafin Saka ya buga kwallon Chiellini yayi kururuwar "Kiricocho" wadda ta kasance kalmar da yan wasa ke amfani da ita wajen yiwa abokan karawar su fatan rashin nasara.
Kiricocho!' - Chiellini claims he 'cursed' Saka before decisive penalty miss in Euro 2020 final
Italy star Giorgio Chiellini has claimed that he put a "curse" on Bukayo Saka before the...