
Bayan Awanni 5 ana tubumarsa, DSS ta saki Ghali Umar Na’abba
Ghali Umar Na'abba, Tsohon kakakin majalisar Wakilai ya amsa gayyatar da DSS suka masa a Abuja yau, Litinin.
Bayan shafe awanni 5 DSS di na tsare dashi yana amsa tambayoyi, an sakeshi inda bayan fitowa daga Ofishin DSS din ya zarce Utako inda Ofishin kungiyar ta NCFRONT yake.
Ana tunanin ya je can dinne dan yiwa abokan tafiyarsa bayanin yanda ta kaya a ofishin DSS din. Ana zargin cewa kalaman da Na'abba yayi na cewa gwanati ta gaza ne suka sa aka gayyaceshi.