
Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasar Ghana ta kame wata ‘yar Najeriya mai shekaru 20 da laifin safarar wasu ‘ yan mata zuwa kasar don yin karuwanci
Jami’an hukumar kula da shige da fice dake kasar ghana, a yankin Tema sun yi nasarar cafke wata mata da ake zargi da yunkurin safarar wasu mata 'yan Najeriya biyu zuwa kasar Ghana da nufin sama musu aiki.
Wadda ake zargin Mai suna Favour Chidi, rahotanni sun tabbatar da cewa, tana gudanar da ayyukanta na karuwanci ne a kasar ta ghana.
Kwamandan hukumar shige da fice dake a yankin Tema Kojo Oppong Yeboah shine ya tabbatar da hakan, a wata sanarwa da ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a kasar.
Sanarwar ta bayyana cewa, wandanda abin ya shafa sun hada da wata budurwa mai shekaru 19 tare da wata budurwar mai shekaru 20.
Kwamandan hukumar ya kuma bayyana cewa, rundunar tai nasarar cafke mai laifin ne ta hanyar bayanan sirri da hukumar ta samu.