
An kai sojoji da ‘yansanda Gidan yarin Ikoyi na Legas bayan yunkurin matasa na fasashi
Rahotanni daga gidan yarin Ikoyi dake birnin Legas sun bayyana cewa wasu fusatattun matasa sun yi yunkurin fasa gidan yarin inda aka ga 'yan gidan yarin na gudu.
Saidai tuni jami'an gidan yarin sun sanar da 'yansanda da sojoji kan abinda ke gudana kuma an kai musu dauki.
Wani shaida ya bayyana cewa ya hango hayaki na tashi a saman gidan yarin kuma ana fito na fito da jami'an tsaron gidan yarin da wanda ake tsare dasu.
Kakakin 'yansandan Legas, Muyiwa Adejobi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kai jamiansu wajan.