
Da Dumi-Dumi:Bidiyo Girgizar kasa ta afkawa kasar Ghana
A daren jiyane aka samu Girgizar kasa a Kasar Ghana me girman maki 4.0.
Shafin Joy online na kasar ya bayyana cewa an ji motsin kasa har sau 3 cikin mintuna 10 da girgizar kasar. Saidai babu sanarwar lalata muhalli ko kuma rasa rai.
Girgizar kasar kamar yanda Hutudole ya fahimta ta farume da misalin karfe 10:40 na daren jiya. Saidai zuwa lokacin hada wannan Rahoto babu sanarwa a hukumance daga kasar kan girgizar kasar data faru.
Kalli bidiyon lamarin a kasa: