fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Giwaye

Yanda Garken Giwaye ke kai hari a Borno

Yanda Garken Giwaye ke kai hari a Borno

Uncategorized
A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyam wasu mazauna garin Rann a yankin karamar hukumar Kala Balge, na kokawa da iftila'in farmakin da wani garken giwaye ke kai musu, Giwayen dai na barnata amfanin gonakinsu inda a wasu lokuta ma su kan yi ƙoƙarin shiga cikin gari. Bayanai dai sun nuna cewa giwayen na shigowa garin ne daga ƙasar Kamaru mai maƙwabtaka kuma sun fi shiga ne a cikin dare. Hukumomin jihar ta Bornon dai sun ce za su tattauna da gwamnatin Kamaru don shawo kan matsalar farmakin giwayen, baya ga matakin da ta ce za ta ɗauka wajen tallafawa wadanda ɓarnar ta shafa.   Matsalar farmakin giwaye a gonaki da kuma gidaje abu ne da aka shafe shekaru ana fama da ita a wasu yankunan jihar Borno, musamman ma wadanda ke kusa da kan iyakoki ƙasas...