
Wani Lauya ya maka Jihohin Jigawa, Kano da sauransu a Kotu inda yace tunda dai sun haramta shan Giya to su dawo da Harajin giya da suka karba
Wani lauya, Sesugh Akume ya maka jihohin da suka haramta shan giya a Najeriya a kotu inda yace yana neman su dawo da kudin harajin giya da aka basu.
Ya saka babban lauya na gwamnatin Tarayya da Hukumar EFCC a cikin wanda yake kara.
Yace wadannan jihohi suna karbar kudi daga gwamnatin tarayya wanda kuma akwai harajin giya a cikinsu. Yace amma kuma sai su rika hana kasuwancin giya da caca suna lalatasu.
Yace misali A Kano, Hisbah na irin wannan abu da kuma Jihar Jigawa. Yace yana so a hanasu saboda kundin tsarin mulkin Najeriya da ba ruwansa da Addini bai haramta ta'ammuli da Giya ba.
Jihohin Arewa da suka haramta ta'ammuli da giya sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Borno, Yobe, Jigawa, Bauchi, Gombe, Zamfara da Niger.
&nb...