
Badaru, Bagudu, Barkiya Sun Bada Gudummawar Naira Miliyan 60 Ga Wadanda Gobara Ta Shafa a Kasuwar Katsina
A ranar Laraba ne gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, da takwaransa na jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, suka ziyarci Gwamna Aminu Masari don yi masa ta’aziyya tare da sauran al’ummar jihar Katsina kan gobarar da ta lakume wasu sassan babbar kasuwar ta Katsina.
Gwamnonin biyu sun sanar da bayar da gudummawar naira miliyan 20 kowannensu a matsayin gudummawar da suka bayarwa don dakile illar gobarar tare da taimaka wa wadanda abin ya shafa.
Sun roki Allah Madaukakin Sarki da ya sake cika duk abin da ya ɓace yayin tashin wutar kuma ya kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.
Hakanan, Sanatan da ke wakiltar shiyyar Katsina ta Tsakiya, Kabir Abdullahi Barkiya, ya ba da gudummawar miliyan N20 ga wadanda bala'in gobara ya shafa a kasuwar ta Tsakiya.
Barkiya ya bayar da gud...