
EFCC ta fara Bincikar Ministan Naija Delta>>Godswill Akpabio
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukukar hana cin hanci ta EFCC tuni ta fara bincikar Ministan Naija Delta, Godswill Akpabio da kuma shugaban hukumar raya yankin ta NDDC, Farfesa Kemebradikumo Pondei kan zargin Almundahanar Kudi.
Hakan ya tabbatane a wasikar da EFCC ta aikewa da wata kungiya me rajin dabbaka kyakyawan Jagoranci da kuma 'yanci karkashin shugabancin Deji Adeyanju.
Kungiyar ta aikewa da EFCC bukatar bincikar Akpabio akan zargin lakume Biliyan 40 kuma tuni EFCC tace ta fara wannan binciken.