
Obaseki ya tsallake tarkon APC kan zargin amfani da takardun Karatu na Bogi inda Kotu ta wankeshi
Babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta wanke gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki kan zargin amfani da takardun karatu na Bogi.
Mai shari'a Ahmed Muhammad da yake karantu hukuncin yace APC data shigar da karar ta kasa bayar da gamsashshiyar Hujja da zata nuna cewa takardun karatun gwamnan na Bogi ne.