
Premier League: Jamie Verdy ya lashe kyautar Golden Boot yayin da Ederson ya lashe kyautar Golden Gloves
Jamie Verdy yayi nasarar lashe kyautar Golden Boot na gasar premier league a wannan kakar yayin da yafi yan wasan gasar cin kwallaye masu yawa duk da abin kunyan da yayi a ranar karshe, shi kuma Edderson yaci kyautar Golden Gloves.
Verdy ya kasa ciwa Leicester City kwallo a wasan da suka buga da Manchester United na samun cancanta a gasar zakarun nahiyar turai a ranar karshe ta gasar premier league, yayin suka gama gasar ana biyar kuma suka tashi wasan 2-0. Amma duk ga haka kwallayen shi 23 sun sa ya lashe kyautar kuma Leicester ta taya shi murna a safin ta na Twitter.
Dan wasan Arsenal Aubameyang ne yayi nasarar zuwa na biyu a cikin yan wasan da suka fi cin kwallaye masu yawa a gasar premier league, yayin da shima Danny Ings ya keda kwallaye 22 sai Raheem Sterling da kwallaye 20.
...