fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Gombe covid19

Wasu mambobi 5 na majalisar jihar Gombe sun kamu da cutar coronavirus/covid-19

Wasu mambobi 5 na majalisar jihar Gombe sun kamu da cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Rahotanni sun bayyana cewa Mambobin majalisar jahar Gombe su kimanin mutum 5 sun harbu da cutar coronavirus/covid. Wata majiya mai tushe ta fadawa Solacebase a ranar Litinin inda kuma shafin Hutudole ya labarto daga majiyar da cewa mambobin suna daga cikin mutum 16  da aka tabbatar sun kamu da cutar Covid-19 a jihar a ranar Lahadi.   Majiyar ta ce daya daga cikin mambobin da suka kamu da cutar ta tabbatar wa wakilinmu cewa mambobi biyar din sun hada da wasu manyan jami’an majalisar. Haka zalika An kuma ruwaito cewa wani memba na majalisar zartarwa na jihar shima ya kamu da cutar coronavirus. Sai dai har yazuwa yanzu kwamitin yaki da cutar Covid-19 bai tabbatar da lamarin kamuwar manyan jami'an gwamnatin jihar ba, harzuwa wannan lokaci.