fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Gombe

Zubar da jinin da ake a Najeriya yayi yawa>>Shugaba Buhari yayi Allah wadai da Rikicin Billiri,  Jihar Gombe

Zubar da jinin da ake a Najeriya yayi yawa>>Shugaba Buhari yayi Allah wadai da Rikicin Billiri, Jihar Gombe

Tsaro
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da rikicin Billiri, Jihar Gombe inda ya bayyana cewa zubar da jinin da ake a Najeriya yayi yawa.   Shugaban kasar ya bayyana cewa, abin takaici ne ganin yanda wasu rikice-rikice da za'a iya magancesu ta hanyar lalama ke komawa tashin  hankali sosai.   Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar kan lamarin inda yace shugaba Buhari yayi Allah wadai da abinda ya faru sannan ya nemi a dauki mataki dan kada rikicin ya yadu.   Shehu quoted the President as expressing “great shock and deep concern” over the incident. The President said, “I’m seriously disturbed by the outbreak of violence in Gombe State and call on the parties involved to exercise maximum restraint to a...
Mutane Uku sun mutu, an kama 10 a yayin zanga-zanga a karamar hukumar Billiri, jihar Gombe

Mutane Uku sun mutu, an kama 10 a yayin zanga-zanga a karamar hukumar Billiri, jihar Gombe

Tsaro
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Gombe, Shehu Maikudi, ya tabbatar da mutuwar mutane uku da ba a san ko su wanene ba yayin da aka kame wasu 10, biyo bayan wata zanga-zanga da kuma sanar da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta yi. Wasu gungun mata sun shiga zanga-zangar lumana kan ikirarin da aka shirya na nuna wani dan takarar da ba a so a matsayin kujerar Mai Tangale bayan rasuwar Abdu Buba Maisheru. Maikudi ya yi magana ne a ranar Asabar lokacin da Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranci wasu mambobin gwamnatin jihar rangadi a karamar hukumar Billiri. Ya ce, “Zuwa yanzu, mun cafke mutum 10 da ake zargi. Kimanin mutane uku suka mutu a yayin faruwar lamarin. ” Yahaya, ya ce, wadanda ke haddasa rikici a cikin al'umma za a hukunta su, ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin dawo d...
Mazan Aure sun yi matukar karanci a jihar Gombe

Mazan Aure sun yi matukar karanci a jihar Gombe

Auratayya
Rahotanni daga jihar Gombe na nuni da cewa wata matsala da ta dade tana ciwa musamman matan jihar tuwo a kwarya shine yanda mazan aure suka yi karanci.   A shekarar 2013, an samu mata kusan sun fita zanga-zanga a jihar Zamfara inda suke kukan rashin Miji. A shekarar 2009 ma matan jihar Kano sun so su yi irin wannan zanga-zanga amma gwamnatin jihar ta dakatar dasu sannan kuma ta shirya aurar dasu.   Saidai matsalar ba'a Arewa maso yamma kawai ta tsaya ba ko kuma matan Musulmai kadai ta ke shafa ba.   A jihar Gombe, Wata Fasto ya koka da cewa mata sun yi yawa amma babu mazan aure. Ya bayyana cewa yanzu matan suna auren Yarbawa saboda a Ajihar mazan sun ki fitowa su auresu. Akwai dai yarbawa da suka dade da zama a jihar Gombe inda sarkin Yarbawan jihar, Abdulr...
Sheikh Bala Lau Ya Yi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Su Yi Gaggawar Hana Kiristoci Kona Masallatai da Dukiyoyin Musulmi A Billiri

Sheikh Bala Lau Ya Yi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Su Yi Gaggawar Hana Kiristoci Kona Masallatai da Dukiyoyin Musulmi A Billiri

Siyasa
...Ya kuma yabawa Gwamnatin jihar Gombe a kokarin da take na dawo da zaman lafiya a Billiri   Shugaban kungiyar wa’azin musulunci ta IZALA Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga jami’an tsaro, musamman hukumar ‘yan sanda, da suyi gaggawar hana kiristoci kona masallatai da dukiyoyin su a garin Billiri dake jihar Gombe.   Shehin Malamin yace,abun takaici ne kwarai, akan batun nada sabon sarki wanda ba’a kai ga sanarwan ba, amma haka al’ummar kiristoci na Garin Billiri suka fito sukayi ta kona masallatai da dukiyoyin al’umnar musulmi ba gaira babu dalili.   Sheikh Bala Lau yace idan an bibiyi tarihin sarautar billiri, musulmi sukayi shekaru dari da uku suna mulki a kasar billiri ba tare da zaluntar kiristoci ba, sai a shekarar 2001 a mulkin marigayi Habu ...
Bidiyon ‘yansandan Najeriya na kallo ana lalata Masallaci a Billiri jihar Gombe amma basu dauki mataki ba

Bidiyon ‘yansandan Najeriya na kallo ana lalata Masallaci a Billiri jihar Gombe amma basu dauki mataki ba

Tsaro
Rahotanni daga Billiri dake jihar Gombe na ci gaba da fitowa dake nuna alamar matsalar tsaro dake da alaka da Mulkin Sarauta wadda ke neman rikidewa ta koma ta addini.   Tsohin Mai na Masarautar, Abdu Buba Maisheru ya hau sarautane bayan Sarki Musulmi ya rasu, kamar yanda Ahmad Muhammad Hussaini daya fito daga jihar ya bayyana. Yace a wancan lokacin Musulmai basu tada hankali ba sukace basu yadda ba. Saidai wanda suke inkarin Sarautarsa sun je kotu.   Yace a yanzu an mikawa Gwamnatin jihar sunayen mutane 3, 2 Musulmai, 1 Kirista wanda dukansu Zasu iya zama sarki. Yace amma Kirostoci suna neman cewa dolene a Nada Kirista Sarautar. Yace maganar gaskiya duka 3n sun cancanta dan haka zabar daya ace shine za'a baiwa Sarautar dole ba daidai bane.   Yace an fara l...
Ana samun ƙaruwar yi wa yara fyaɗe a jihar Gombe

Ana samun ƙaruwar yi wa yara fyaɗe a jihar Gombe

Tsaro
Masu fafutukar kare haƙƙin mata da ƙananan yara sun alaƙanta ƙaruwar cin zarafin mata da ake samu a jihar Gombe da jan ƙafar da ake yi a shari'o'in masu aikata lalata. Wani bincike na baya-bayan nan ya ce Gombe na cikin jihohin da ke sahun gaba a Najeriya a yawan cin zarafin yara. Haka kuma, an danganta ƙaruwar lamarin da rashin ƙwararan dokokin hukunta masu aikata laifin a jihar. Kwamishinan ƴan sandan jihar Maikuɗi Shehu ya ce kusan kullum suna samun rahoton fyaɗe musamman na ƙananan yara. Ya ce "sai ka ga dattijo ya lalata ƙaramar yarinya. Wannan ba ya rasa nasaba da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Shi ya sa muke duba yadda za mu shawo kan wannan matsala" Wata mai fafutukar kare haƙƙin,Hajiiya Fati Usman Kulani ta ce idan ba a yi wa tufkar hanci tun yanzu ba, nan gaba abun ...
Gwamnatin Jihar Gombe Ta Amince Da Biliyan N3.24 Domin Sanya Fitilun Titi Masu Amfani da Hasken Rana

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Amince Da Biliyan N3.24 Domin Sanya Fitilun Titi Masu Amfani da Hasken Rana

Siyasa, Uncategorized
A jiya ne Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da Naira biliyan 3 da miliyan 244 don sanya fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a cikin garin na Gombe. Kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar, El-Hassan Ibrahim Kwami, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwar jihar, ya ce aikin da zai kai kimanin kilomita 71 na titunan garin Gombe za a kammala shi cikin watanni uku. Ya ce a matsayin wani bangare na aikin, za a horar da matasa kan yadda ake sarrafa fitilun bayan an kafa su, ya kara da cewa za a yi kage da sauran ayyukan da ake bukata a Gombe don tabbatar da abubuwan cikin gida da samar da ayyukan yi. Kwami ya ce mahimmancin horon shi ne tabbatar da dorewa saboda dan kwangilar zai gudanar da aikin na tsawon shekaru biyar...
Gwamnatin Tarayya ta raba kayan aikin gona kyauta da iri mai inganci ga kananan manoma a jihar Gombe

Gwamnatin Tarayya ta raba kayan aikin gona kyauta da iri mai inganci ga kananan manoma a jihar Gombe

Uncategorized
Gwamnatin Tarayya ta raba kayan aikin gona kyauta da iri mai inganci ga kananan manoma a jihar Gombe, a cewar wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ranar Lahadin data gabata daga Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara. Sanarwar ta fito ne daga Mista Ezeaja Ikemefuna, babban jami’in yada labarai na ma’aikatar aikin gona wanda ya ambato karamin Ministan, a ma’aikatar, Mustapha Shehuri, wanda ya bayyana manufar samar da kayayyakin ga kananan manoma da cewa cigaba ne da zai bunkasa harkar Noma da samar da abinci mai gina jiki tare da samawa matasa aikin yi. Ministan yayin gabatar da taron a harabar ofishin ma’aikatar da ke Gombe, ya ce hakan na daga cikin matakan rage radadi da cutar covid-19 ta haifar da Kuma ambaliyar da ta lalata gonaki. Haka zalika ya sha Al"washin cigaba da tallafawa...
Hukumar Kiyaye hadura FRSC ta gargadi masu baiwa yara damar tuka ababan hawa

Hukumar Kiyaye hadura FRSC ta gargadi masu baiwa yara damar tuka ababan hawa

Tsaro
Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), reshen jihar Gombe, ta yi gargadi game da baiwa yara kanana damar tuki a jihar. Mista Ibrahim Hassan, jami'in hulda da jama'a na hukumar FRSC a jihar shine ya yi wannan gargadin a ranar Asabar A lokacin da Jami'an hukumar ke kokarin wayar da kan masu ababen hawa a garin Zambuk, dake karamar hukumar Yamaltu-Deba da ke jihar. Hukumar ta ce  ta lura a yanzu wasu na baiwa kananan yara damar tuka Babur mai kafa uku kai harma da motocin haya wanda a cewar ta hakan ya ci karo da tsarin hukumar na abbatar da kiyaye lafiya da kuma dokar hanya. Bugu da kari hukumar ta kuma gargadi direbobi da su kaucewa ta'ammuli da miya gun kwayoyi a yayin da suke gudanar da tuki NAN