
Gwamnoni 4 daga Arewa na son Goodluck Jonathan ya zama shugaban kasa a 2023
Manyan 'yan jam'iyyar APC daga jihar Bayelsa sun fara shirye-shiryen ganin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya dawo a shekarar 2023.
Kuma suna samun goyon bayan wasu gwamnoni 4 daga Arewacin Najeriya akan wannan aniya, kamar yanda The Nation ta ruwaito.
Wata Majiya ta gayawa kafar cewa gwamnonin na jira maganar takarar Jonathan ta fara fitowa daga Kudu ne kamin su saka baki.
Goodluck Jonathan dai bai karyata maganar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba sannan kuma bai ce zai tsaya din ba.
The four Northern governors backing the return of Jonathan in 2023 wanted the South-South to start the campaign first while they play a supportive role in midwifing the process. They want the argument to originate from their zone of interest”.