
Saboda Tsoron Allah shugaban Najeriya na sakawa Titi a kasata sunansa>>Shugaban kasar Guinea Bissau
Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Embalo ya godewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari saboda taimakon da yake bashi da kuma shawara irin ta da da uba da yake bashi tun kamin zaben sa har kuma aka zabeshi shugaban kasa.
Ya kara da cewa ya sakawa wani titi a babban birnin kasarsa, Bissau sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari saboda tsoron Allah da gaskiya da kuma dattijan taka ta shugaba Buhari.
Shi kuwa shugaban kasar, Senegal Macky Sall jinjinawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi saboda yanda yake bada himma wajan yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi.
Ya kuma bayyana cewa yana jinjinawa shugaban kasar saboda goyon bayan da yake baiwa Kungiyar ECOWAS wajan dawo da zaman lafiya.
Ya bayyana cewa sun kuma tattauna maganar tattalin tsaro da h...