
Coronavirus: Masu zanga-zanga sun tilasta bude Masallatai a Guinea
Masu zanga-zangar adawa da killace jama’a a gida domin yaki da annobar coronavirus a Guinea, sun yi nasarar tilasta bude Masallatan da aka rufe na makwanni a Conakry, babban birnin kasar.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan arrangamar da aka yi tsakaninsu da jami’an ‘yan sanda, abinda yayi sanadin kashe mutane 7 dake adawa da shingen hana zirga-zirgar da jami’an tsaron suka kafa a sassa daban daban na birnin Conakry.
Tun daga karshen watan Maris hukumomin Guinea suka sanya rufe Masallatan a matsayin jerin matakan da suka dauka na dakile yaduwar annobar coronavirus a kasar, wadda kashi 80 na jama’arta Musulmai ne.
Shaidun gani da ido sun ce tarin jama’a suka bude Masallacin garin ‘Kamsar’, suka kuma wanke shi kafin gudanar da sa...