
An Nada Farfesa Mu’azu Gusau A matsayin Mataimakin shugaban jami’ar tarraya ta jihar Zamfara
Jami'ar Gwamantin tarayya dake Gusau a jihar Zamfara ta samu sabun mataimakin shugaban jam'ar Farfesa Mu'azu Gusau.
Sanarwar Nadin ta fito ne daga bakin jami'in yada labarai na jami'ar Umar Usman.
A cewar Sanarwar, Farfesa Mu'azu zai kama aiki ne daga ranar 10 ga watab Fabrarun sabuwar shekarar 2021 idan Allah ya kaimu.
Farfesa Mu"azu Gusau farfesa ne a fanni ilimin Toxicology wanda ke koyarwa a jami'ar Usman Danfodiyo dake jihar sokoto, Muazu, wanda ya samu digirin digirgir a Jami’ar Surrey ta Ingila, zai karbi aikin ne daga hannun Farfesa Magaji Garba wanda ya koma tsohuwar Jami’ar sa ta Ahmadu Bello dake zariya.