fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Gwal

GWAMNATIN ZAMFARA TA GABATAR DA MA’ADANAI WADANDA AKA HAKO A CIKIN JIHAR CIKIN WATA BIYU

GWAMNATIN ZAMFARA TA GABATAR DA MA’ADANAI WADANDA AKA HAKO A CIKIN JIHAR CIKIN WATA BIYU

Siyasa, Uncategorized
Albishirinku al'ummar jihar Zamfara ku kalli irin kokarin da Gwamna Matawalle yake yi wa al'ummar wannan jihar. Don tabbatar da cewa jihar Zamfara mun dogara da kanmu. Kuma wannan ma'adanan dukka an same su ne a cikin wannan jihar ta mu cikin kwanaki kadan. Allah mun gode maka da ka bamu Gwamna mai kishinmu wanda yake komai don tabbatar da adalci da gaskiya. Allah ya kara zama jagoranka Mai Girma Gwamna.
Jihar Zamfara ta samar da Rumbun tara Gwal

Jihar Zamfara ta samar da Rumbun tara Gwal

Siyasa
Jihar Zamfara dake Arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da samar da Rumbun tara Gwal. Jihar ta sanar da hakane ta bakin kwamishinan kudinta, Rabiu Garba. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da gwamnan jihar, Bello Matawalle ya je ya gabatarwa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari gwaldin da aka hako a jihar.   Kwamishinan yace duk da gwamnatin tarayya ta hana hakar gwal amma sun samu nasarar sayen gwal dinne a hannun masu hakar gwal din dake da lasisi, yace yanzu suna da Gwal Kilo 30 kuma zasu ci gaba ta tarashi har zuwa lokacin da bukatarsa zata taso.   Yace nan gaba idan aka dawo da hakar gwal din zasu rika samun kudin shiga daga harajin masu hakarsa sannan kuma daga gwamnatin tarayya.   Zamfara government on Tuesday, said it has started its gold res...
Hotuna: Shugaba Buhari ya sai Gwal na farko da aka sarrafa a Najeriya kan Miliyan 268

Hotuna: Shugaba Buhari ya sai Gwal na farko da aka sarrafa a Najeriya kan Miliyan 268

Siyasa
A yaune shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin Sarrafa Gwal a fadarshi ta Villa. Sannan kuma shugaban kasar ya sai gwal din wanda shine na farko da aka sarrafa a Najeriya.   Gwaldin me nauyin Kg 12.5 shugaban kasar ya sayeshine ta hannun babban bankin Najeriya, CBN akan Naira Miliyan 268.6, kamar yanda hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ya bayyana. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1283754043224002565?s=19 Yace an sarrafa gwaldinne bisa ka'idojin sarrafa gwal na Duniya sannan kuma zai zama a cikin Lalitar Gwamnati, ya zama kudin kasa kenan.
Hotuna: An Gina Otel Din Zinari Na Farko A Duniya A Kasar Vietnam

Hotuna: An Gina Otel Din Zinari Na Farko A Duniya A Kasar Vietnam

Siyasa
Hotel din Gwal na farko da aka gina a kasar Vietnam ya fara aiki. Otel din mai hawa 24, Komai da aka sanya a ciki ya kasance na zinari, kamar su kujeru, kofi, cokali,kayan danki da wasu abubuwa, an kashi dala miliyan 200, kimanin naira biliyan 78 kuma an dauki shekaru 11 ana gina shi.   Hatta dakin wanka da abubuwan ciki duk na zinari ne. Otel din da aka sanya mashi suna, Dolce Hanoi Golden Lake Hotel, yana cikin babban birnin Hanoi, kusa da wani kogi kuma otel din yana da dakuna guda 400. Ana biyan dala 250, kimanin naira 97,000 a kowane kwana a otel din, sannan akwai bangaran da mutane za su iya ansa haya na shekaru. Philip Park, Wanda ya fito daga yankin Koriya ta kudo, ya ce; " lokacin dana zo otel din, naji kaina tamkar wani sarki". Nyugen huu ...
Wasu masu fada aji na matsawa gwamnati akan ta saki ‘yan kasar Chinar da aka kama suna hakar ma’adanai ba bisa ka’idaba

Wasu masu fada aji na matsawa gwamnati akan ta saki ‘yan kasar Chinar da aka kama suna hakar ma’adanai ba bisa ka’idaba

Uncategorized
Ministan tama da karafa, Olamikekan Adegbite ya bayyana cewa suna fuskantar matsi daga wasu masu fada aji akan sakin 'yan kasar China da aka kama suna hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.   An kama 'yan kasar China 2 a jihar Zamfara suna hakar Gwal wanda tuni gwamnatin tarayya ta haramta hakan saboda yanda yake da alaka da harkar 'yan bindiga da suka addabi jihar.   Hakanan a jihar Osun a kama mutane 27 da ke hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba wanda 17 daga ciki 'yan kasar Chinane, akwai 'yan Burkina Faso da Senegal da 'yan Najeriya.   Ministan a ganawar da yayi da manema labarai yace yawancin 'yan kasar wajen suna zanene a Najeriya ba bisa Ka'ida ba.   Yace kuma akwai manyan mutane a gwanatocin jihohi da cikin jami'an tsaro da sarakunan gargaji...