
Babban taron APC: “Bana tsoron odar kotu”>> Gwamnan jihar Kano, Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa baya tsoron barazanar da kotu keyi akan babban taron da zasu gudanar na APC ran 26 ga watan uku, bayan ta bukaci su daga taron.
Inda ya tabbatarwa masu ruwa da tsaki a taron cewa komai zai tafi kamar yadda suka tsara, domin a fadin Afrika ba jam'iyya mai kafin tasu saboda haka zasu iya shawo kan komai.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a jihar Abuja, inda ya kai ziyara babban gidan sakateriya.