fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Tag: Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

“Ku zabi PDP don ta ceto Najeriya daga mawuyacin halin datake ciki”>> Tambuwal

“Ku zabi PDP don ta ceto Najeriya daga mawuyacin halin datake ciki”>> Tambuwal

Breaking News, Siyasa
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal mai neman takarar shugabanci a jam'iyyar PDP, yayi kira ga al'ummar Najeriya cewa su zabi PDP domin ta ceto kasar a mawuyacin hali data ciki. Tambuwal ya fadi hakan ne a gidan sakateriyar PDP dake jihar Kaduna a ranar asabar, inda ya gudanar da taro tare da membobin jam'iyyar. Tsohon gwamnan Sokoto Bafarawa ya halacci taron dare sauran manyan jam'iyyar PDP, kuma Tambuwal ya kara da cewa jihar Kadune ta PDP ce domin sunada kansiloli bila adadin a jihar.
Makaman daken hannun farar hula sun fi na jami’an tsaro yawa, Ya kamata a saka dokar kisa ko daurin rai da rai akan duk wanda aka samu da makami>>Gwamna Tambuwal

Makaman daken hannun farar hula sun fi na jami’an tsaro yawa, Ya kamata a saka dokar kisa ko daurin rai da rai akan duk wanda aka samu da makami>>Gwamna Tambuwal

Tsaro
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya nuna damuwa kan yanda ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a kasarnan inda ya bada shawarar da yace ita kadai ce zata kawo zaman lafiya a kasarnan.   Gwamna Tambuwal yayi wannan maganane a yayin da yake ganawa da dalibai da kuma matasa akan harkar tsaro. Ya bayyana cewa ya kamata a majalisar tarayya da gwamnatin tarayya su saka dokar daurin rai da rai ko kuma kisa ga duk wanda aka samu da makami.   Yace yanda za'a yi abin shine a baiwa duk wani me dauke da makami damar ya je ya mai rijista idan kuma ba za'a iyawa makamin nashi rijista ba to ya mikawa gwamnatishi a mayar mada da kudinsa.   Daga nan kuma sai a saka dokar cewa duk wanda aka kama da makami to daurin rai da rai ne ko kuma kisa.   ...