fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Gwamna Badaru

JIGAWA: Majalisa ta dakatar da mamban da ya ingiza matasa suka yi wa tawagar gwamna dabanci

JIGAWA: Majalisa ta dakatar da mamban da ya ingiza matasa suka yi wa tawagar gwamna dabanci

Siyasa
Kakakin majalisar Jigawa ya bayyana a zauren majalisar cewa majalisar ta dakatar da dan majalisar dake wakiltar Gumel, Sani Isyaku a dalilin zargin yi wa tawagar gwamna dabanci.   Kakakin majalisar Idris Garba ya bayyana cewa Sani Isyaku ya ingiza matasa su yi wa gwamnan jihar Muhammadu Badaru dabanci.   Garba ya ce hakan karya dokar majalisar ne dama dokar kasa.   A dalilin haka majalisar ta dakatar da shi na tsawon sai wadda hali yayi. Wato ba ranar dawowa, sannan kuma ya umarce shi da ya maido da duk wani abu na majalisa dake hannun sa.   Bayan haka kuma ya kara da cewa majalisar ta kafa kwamiti domin bin diddigin abin da ya faru.   Sai dai kuma hakan bai yi wa dan majalisa Umar Danjani dadi ba duk da ba jam’iyyar su daya da Isyaku ...