
A kullun Burina a yi zaben gaskiya>>Shugaba Buhari ya taya gwamna Obaseki Murna
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan da aka gudanar a jihar.
Hakan ya fitone daga kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu inda yace a kullun burinshi shine a yi zabe na gaskiya.
Yace idan babu zaben gaskiya to siyasar mu da karfin Ikonmu zai raunana. Yace Dimokradiyya ba zata cika ba sai an tabbatarwa da mutane abinda suka zaba ba tare da katsalandanba.
Shugaban a karshe ya jinjinawa jama'ar jihar Edo, jami'an tsaro da 'yan takarar da suka fafata bisa zaben da aka yi cikin kwanciyar hankali.