
Yanzu-Yanzu: Na sa a sake zaben sabbin wanda za’a baiwa sarkin Zazzau bayan na soke sunayen farko
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya tabbatar da soke sunayen farko da masu nada sarkin Zazzau suka fitar.
Gwamnan yace sunayen farko ya soke sune saboda ba'a saka sunayen mutane 2 dake neman sarautar ba.
https://twitter.com/GovKaduna/status/1311364131828707332?s=19
Yace ya bada umarnin a sake zaben wasu sabbin sunayen. Gwamnan ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumuntar Twitter.