Wadannan hotunan 'ya'yan dan uwan gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne wanda ake kira da Bashir El-Rufai da suka dauki hankula a shafukan sada zumunta.
Shafin Munah El-Rufai ne ya wallafa hotunan wanda kuma tuni mutane suka ta bayyana mabanbNta ra'ayoyi akai.
Shugaban kungiyar matasan Arewa,Shattima Yarima ya bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna,Malam Nasir Ahmad El-Rufai a rude yake kan maganar tsaro a jiharsa.
Yace bawai a Kudancin Kaduna kadai ake samun matsalar tsaro ba harma Tsakiyar Kaduna i da yace babu inda mutane suka tsira. Yace matsalar gwamnan Kaduna shine yana hada abu uwa da yawa a lokaci daya yace zaiyi wanda hakan sai yasa ya shiga Rudani ya rasa abinda ma ya kamata yayi. Yace irin hakan na faruwa ne idan mutum na tunain shi kadaine ya fi kowa wayau da Ilimi.
Yace abinda gwamnan ya kamata yayi shine ya zauna da shuwagabannin al'umma dan a tattauna yanda za'a shawo kan wannan matsalar.
Ya kuma jawo hankalin gwamnatin tarayya kan cewa ya kamata ta shigo cikin lamarin dan samar da karin jami'an tsaron ...