fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Gwamna Rotimi Akeredolu

Gwamnan Jihar Ondo, Akeredolu Ya Warke Daga Cutar Korona

Gwamnan Jihar Ondo, Akeredolu Ya Warke Daga Cutar Korona

Kiwon Lafiya
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo bayan gwaji ango baya dauke da cutar korona. Gwamnan ya kamu da cutar korona kwata-kwata makon da ya gabata. Gwamna Akeredolu a cikin wata sanarwa da aka watsa ta jihar baki daya ya ce bayan ya kwashe kwanaki a kulle, Likitoci sun tabbatar masa da cewa baya dauke da cutar bayan gudanar da gwajin sau biyu. Gwamnan ya bukaci mazauna jihar da su yi taka-tsantsan game da kwayar cutar. Ya ce duk da kalubalen, Gwamnati za ta ci gaba da bayar da himma don dakile matsalar.
Ha’ila yau, mataimakin gwamnan Ondo, Ajayi ya sake nada mataikansa da Gwamna Akeredolu ya kora

Ha’ila yau, mataimakin gwamnan Ondo, Ajayi ya sake nada mataikansa da Gwamna Akeredolu ya kora

Siyasa
An kori mataimakan Mataimakin Gwamnan kwana biyu bayan da shugabansu ya yi bar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP). A cikin kiran waya da babban sakataren yada labarai na ofishin mataimakin gwamnan, Okeowo ya tabbatar da cewa mataimakin Gwamnan ya sake nada dukkan mataimakansa da Gwamnan Jihar ya sora. "Eh, gaskiya ne cewa gwamna ya sanar da korar mu, amma babu wani abin damuwa, kamar yadda mataimakin gwamnan ya sake mayar damu aiki." A ranar lahadin da ta gabata, Ajayi ya fice daga jam’iyyar APC, sakamakon takaddama da ta kaure tsakanin sa da gwamnan, sannan daga baya ya dauki katin membobin PDP.
Hotuna:Shugaba Buhari ya gana da gwamnan Ondo

Hotuna:Shugaba Buhari ya gana da gwamnan Ondo

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya gana da gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a fadarshi ta villa dake babban birnin tarayya, Abuja.   Ganawar tasu ta kasance a yau,Talata, kamar yanda sanarwa ta fito daga fadar. Gwamna Akeredolu ya je nunawa shugaba Buhari fom din sake tsayawa takarar gwamnan jihar sa ne a zango na 2. https://twitter.com/NigeriaGov/status/1272867963641696256?s=19 An ga shugaban kasar da gwamnan rike da Fom din ana daukarsu hotuna.