fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Tag: Gwamna Yahaya Bello

“Kasancewarka daya daga cikin mutanen da suka kirkiri jam’iyyar APC ba zai sa a baka tikiti ba”>>Gwamna Bello Yahaya ya fadawa Tinubu

“Kasancewarka daya daga cikin mutanen da suka kirkiri jam’iyyar APC ba zai sa a baka tikiti ba”>>Gwamna Bello Yahaya ya fadawa Tinubu

Breaking News, Siyasa
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana cewa baya tsoron mayan yan siyasar dake neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar APC. Inda yace yanada yakinin cewa duk zai doke su kuma shi jam'iyyar APC zata tsayar a matsayin dan takararta a shekarar 2023. A karshe ya kara da cewa kasancewar Tinubu daya gada cikin mutanen da suka kirkiri jam'iyyar APC ba zai sa a bashi tikiti ba, saboda haka ba zai yi kasa a gwiwa ba.
“Bana tsoron Tinubu da Osinbajo’ duk zan doke su a zaben shekarar 2023”>>Yahaya Bello

“Bana tsoron Tinubu da Osinbajo’ duk zan doke su a zaben shekarar 2023”>>Yahaya Bello

Breaking News, Siyasa
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cew baya tsoron duk wa'yanda ke neman takarar shugabancin Najeriya karkashin tutar APC. Wasu daga cikin masu neman takarar shugabancin karkashin jam'iyyar APC sun hada da tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo. Amma duk da haka Bello Yahaya ya bayyana cewa baya tsoronsu kuma yanada yakinin cewa shine zai yi nasarar lashe zaben a shekarar 2023.
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana matukar Kaduwa game da mutuwar tsohon Ministan Shari’a Abdullahi Ibrahim (SAN)

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana matukar Kaduwa game da mutuwar tsohon Ministan Shari’a Abdullahi Ibrahim (SAN)

Uncategorized
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana matukar kaduwa game da mutuwar tsohon Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Tarayya Abdullahi Ibrahim (SAN), yana mai bayyana rasuwarsa a matsayin rashi ne ga kasar da jihar baki daya. Mirgayin Dan kabilar Igala ne wanda ya fito daga yankin gabashin jihar Kogi, ya rasu ne a ranar Lahadi 24 ga watan Janairun 2021, kuma shine SAN na farko daga Arewacin Nijeriya haka kuma ya yi aiki a matsayin Babban Lauyan Tarayya A tsakanin shekarar Alif 1997 da kuma Alif 1999. Sakon ta'aziyyar ya fito ne daga bakin, Babban Sakataren yada labaran na gwamna Bello, Onogwu Muhammed wanda ya fitar, inda ya bayyana marigayin Abdullahi a matsayin kwararren masanin shari’a kuma mai aiki da kwarewa.
Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya Jajantawa Iyalan wadanda hadarin mota ya rutsa dasu

Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya Jajantawa Iyalan wadanda hadarin mota ya rutsa dasu

Uncategorized
Wani Mummunan hadarin mota da ya afku a jihar kogi a kauyan Akpata da ke karamar hukumar Lokoja na jihar yayi sanadin mutuwar mutane 14 tare da jikkata wasu da dama. An rawaito cewa, Hadarin ya faru ne lokacin da wata mota dauke da fasinja tai taho mugama da wata motar daukar kaya dauke da siminti lamarin da yayi sanadin salwantar rayukan mutum 14. A wani sakon jaje da Gwamnan Jihar Yahaya Bello ya aikewa wadanda lamarin ya rutsa dasu ta hannun kwamishinan jihar Kingsley Fanwo ya nuna matukar damuwarsa tare da yin kira da hukumar Kiyaye hadura ta jihar kan ta tsaurara tsaro da sa'ido a kan hanyoyin jihar.
Bidiyo Shugaba Buhari Waliyyi ne, Soyayyar da jama’a ke masa daga Allah ne>>Gwamna Yahaya Bello

Bidiyo Shugaba Buhari Waliyyi ne, Soyayyar da jama’a ke masa daga Allah ne>>Gwamna Yahaya Bello

Uncategorized
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin mutum na musamman wanda bashi da damuwa.   Yace shugaban kasar waliyyi ne kuma yana da kyakykyawar zuciya.   Yahaya Bello ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ji yana cewa zuciyar shugaban kasar Farace tas. https://twitter.com/DoubleEph/status/1329445911890698240?s=19
Gwamnan Bello ya kalubalanci cibiyar yaki da cututtuka ta kasa NCDC da cewa mutuwar Babban Al’kalin jihar ba Korona bace

Gwamnan Bello ya kalubalanci cibiyar yaki da cututtuka ta kasa NCDC da cewa mutuwar Babban Al’kalin jihar ba Korona bace

Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nuna rashin yarda da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya NCDC game da musabbabin mutuwar Babban Alkalin jihar, Mai shari’a Nasir Ajana. Mai shari'a Ajana ya mutu a ranar Lahadin da ta gabata a cibiyar kebewa dake Gwagwalada COVID-19. Gwamnan, wanda yake magana a yayin addu'o'in ranar uku ga mamacin a ranar Talata, ya ce marigayi Babban Alkali ya mutune amma ba cutar Korona ce ta kashe shiba inda ya bukaci jama'a da kada su danganta mutuwarsa da komai. Gwamnan ya bayyana marigayi CJ a matsayin mutumin kwarai da kuma mai son zaman lafiya. Daman ba tun yanzu ba gwamanan jihar ke hawa dokin naki kan yadda cibiyar yaki da cututtuka ta kasa ke tafiyar da lamuranta akan rahotanin cutar Coronavirus a kasar, inda ake jiyo aman gwamanan na suka tare da...
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello yayi ikrarin cewa nan bada jimawa ba gwamnonin jam’iyyar PDP 10 zasu canza sheka zuwa jam’iyyarsa ta APC

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello yayi ikrarin cewa nan bada jimawa ba gwamnonin jam’iyyar PDP 10 zasu canza sheka zuwa jam’iyyarsa ta APC

Siyasa
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa kwanan nan wasu abokanan sa gwamnonin PDP zasu kama jam'iyyar APC.   Da yake zantawa da tashar talabijin ta Channel Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa nan gaba kadan wasu abokanan sa gwamnonin jam'iyyar Adawa ta PDP su akalla 10 zasu dawo jam'iyyarsa mai mulkin Najeriya wato APC.   Da yake mayar da amsar tambayar cewa ko shin jama'iyyar APC zata durkushe bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kujerar mulki a shekarar 2023, sai ya ce kokadan illama jam'iyyar APC zata kara karfine.   Haka zalika Gwamnan ya bayyana takaicin sa na ficewar gwamnan jihar Edo Obadeki daga jam'iyyar APC inda ya sha al'washin cewa lalle nan gaba zaiyi komayya cikin jam'iyyar sa ta asali APC.  
Babu wani rikici dake damun jam’iyyar mu, akwai gwamnonin PDP 10 ma da zasu dawo APC>>Gwamna Yahaya Bello

Babu wani rikici dake damun jam’iyyar mu, akwai gwamnonin PDP 10 ma da zasu dawo APC>>Gwamna Yahaya Bello

Siyasa
Gwamnan jihar Kogi,Yahaya Bello ya bayyana cewa akwai gwamnonin PDP 10 da zasu koma APC nan ba da jimawa ba.   Gwamnan ya bayyana hakane a hirar da yayi da gidan Talabijin na Channelstv inda yace jam'iyyar su bata cikin rikici. Yace abinda aka gani a makwannin da suka gabata, wata 'yar matsala ce ta faru tsakanin 'yan uwan juna dake jam'iyyar kuma saka bakin shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya warware matsalar.   Yace nan gaba kadan gwamnonin PDP 10 zasu koma APC din kuma a jira za'a ga tabbatar wannan bayanin nashi.
Ina Alfahari da kai>>Shugaba Buhari ya gayawa gwamna Yahaya Bello

Ina Alfahari da kai>>Shugaba Buhari ya gayawa gwamna Yahaya Bello

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana alfahari da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.   Ya bayyana hakane a cikin sakon taya gwamnan murnar cika shekaru 45 da yayi a yau, Alhamis, 18 ga watan Yuni. A sakon da shugaba Buhari ya fitar ta hannun me magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya bayyana gwamna Yahaya Bello a matsayin dan Jam'iyyar APC me matukar biyayya.   Shugaba Buhari yace yana taya gwamnan murna yanda ya samu dama cikin shekarun kuruciya yana bautawa jama'aishi.