Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero Tare Da Mai Martaba Sarkin Gombe Alh. Abubakar Shehu Abubakar III a gurin Ta’aziyar mahaifiyar Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar Maje.
Allah yayi mata Rahama.
Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Muhammad Abubakar ya ba da kyautar motar bas mai daukar mutane 36 ga kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Stars FC.
Kyautar ta zo daidai da kudirin da gwamnan ke yi don taimaka wa ƙungiyar wajan kai bantanta a kakar wasan kwallan kafa na kasa.
Shugaban kungiyar Abubakar Sadik ya gode wa gwamnan bisa goyon baya da kwarin gwiwa da yake nuna wa kungiyar, sannan ya kara da cewa motar za ta kara musu kwarin gwiwa don cimma kaiwa wani matsayi mai kyau a kakar wasan.
Daruruwan wadanda ambaliya ruwa ta shafa A karamar hukumar Hadejia a cikin jihar Jigawa suna koka da mummunan halin da suke ciki a cibiyoyin su.
A cewarsu, gwamnatin jihar ta yi watsi da su, a sakamakon hakan ya janyo wadansun su na mutuwa sabuda yunwa da yawan rashin lafiya a sanadin cututtuka da suke addabarsu.
A wata Sanarwa da Gidauniyar tallafawa mata da marayu ta fitar a ranar Asabar ta roki gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki da su tausaya tare da taimakawa wadanda Ambaliyar ta shafa domin cire su daga kuncin da suke ciki.
Kakakin majalisar Jigawa ya bayyana a zauren majalisar cewa majalisar ta dakatar da dan majalisar dake wakiltar Gumel, Sani Isyaku a dalilin zargin yi wa tawagar gwamna dabanci.
Kakakin majalisar Idris Garba ya bayyana cewa Sani Isyaku ya ingiza matasa su yi wa gwamnan jihar Muhammadu Badaru dabanci.
Garba ya ce hakan karya dokar majalisar ne dama dokar kasa.
A dalilin haka majalisar ta dakatar da shi na tsawon sai wadda hali yayi. Wato ba ranar dawowa, sannan kuma ya umarce shi da ya maido da duk wani abu na majalisa dake hannun sa.
Bayan haka kuma ya kara da cewa majalisar ta kafa kwamiti domin bin diddigin abin da ya faru.
Sai dai kuma hakan bai yi wa dan majalisa Umar Danjani dadi ba duk da ba jam’iyyar su daya da Isyaku ...