fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Gwamnan Kaduna

Tankokin dakon man fetur 11 sun kone a wani gareji da gobara ta tashi a Kaduna

Tankokin dakon man fetur 11 sun kone a wani gareji da gobara ta tashi a Kaduna

Uncategorized
Motocin dakon man fetur 11 sun kone a ranar Talata lokacin da gobara ta kama wani garejin ajiye motoci a Anguwan Mu’azu a Kaduna. Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Abdulahi Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin. Shugaban KADSEMA, wanda ya je wurin domin tantance yadda barnar ta kasance, ya ce lamarin gobarar ya haifar da gano wasu ayyukan bata gari da suka hada da kayayyakin mai a yankin. Ya ce hukumar za ta binciki sa hannun mazauna garin da kuma mambobin kungiyar a cikin irin wadannan ayyukan da ake zargin sun haifar da tashin gobarar. Shaidun gani da ido sun sanar cewa wasu mutane kalilan sun samu raunuka kuma an garzaya da su asibiti don kulawa.
El-Rufa’i yayi Alhini yayin da ‘yan bindiga suka kashe wata mai ciki wata bakwai

El-Rufa’i yayi Alhini yayin da ‘yan bindiga suka kashe wata mai ciki wata bakwai

Tsaro
Gwamna Nasir El-Rufai ya jajantawa mijin wata mata mai cikin wata bakwai da aka kashe, Malam Musa Adamu, wanda wasu ’yan bindiga suka kashe a kan hanyar Kaduna zuwa Brinin a karamar Hukumar Chikun da ke jihar ranar Lahadi. Gwamnan, wanda ya yi addu’ar Allah ya jikan ran Aisha, ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a harin. Kwamishinan, Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ya bayyana cewa, duk da haka, jiragen saman sun gudanar da aiyukan dauke da makamai a Sabon Birni, Albasu, Doka, Kerawa, Rikau, Galadimawa, Kidandan, Ngede Allah, Dogon Dawa, Takama, Damari, Saulawa, Yadi, the Kuduru-Ungwan Yako da sauransu. Sanarwar ta kara da cewa wadannan wurare sun hada da kananan hukumomin Birnin Gwari, Gi...
Kungiyar ‘yan kasuwa A jihar Kaduna sun roki gwamnatin jihar data tsawaita musu wa’adin data ba su na rusau

Kungiyar ‘yan kasuwa A jihar Kaduna sun roki gwamnatin jihar data tsawaita musu wa’adin data ba su na rusau

Kasuwanci
Kungiyar ‘Yan Kasuwa ta kasa (MATAN) ta roki Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna da ya ba su isassun lokaci kafun shirin gwamnatin jihar na rusa shaguna 6,000 dake Kasuwar Ungwan Rimi a Kaduna. Alhaji Jamilu Abbas, Shugaban kungiyar shine yayi wannan rokon a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce cutar COVID-19 hakaki ta shafi 'yan kasuwa dadama tare da kasuwancinsu. Abbas ya ce "duk da cewa kungiyar 'yan kasuwan, na sane da shirin sabunta birane na gwamnati jihar, amma ya kamata a ba da karin lokaci ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa. inji shi  
Yan bindiga sun yi garkuwa da uwa mai shayarwa, mata uku, da manoma 11 a jihar Kaduna

Yan bindiga sun yi garkuwa da uwa mai shayarwa, mata uku, da manoma 11 a jihar Kaduna

Tsaro
Wasu ‘yan fashi sun sace manoma 16, ciki har da yara da mata a kauyen Uduwa, a kan babbar hanyar Birnin Gwari a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna. Wadanda 'yan bindigar suka sace za su je gona ne lokacin da lamarin ya faru da sanyin safiyar Asabar. Wasu rahotanni sun ce wasu mutane hudu sun samu raunuka daga harbin bindiga kuma an yi watsi da su yayin da ‘yan bindigar suka tafi tare da mutane 16, wadanda‘ yan gida daya ne. An gano cewa wasu daga cikin wadanda aka harba din an garzaya da su zuwa asibiti a cikin garin Kaduna don kula da su. Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wanda shi ne shugaban iyalen, Malam Yakubu Barauni, ya fada wa manema labarai a ranar Lahadi cewa 'yan ta'addan sun harbe shi a kafafunsa biyu. Barauni ya ce daga cikin wadanda aka s...
Mutane 2 sun mutu a wani sabon hari da aka kai Zangon Kataf, Kaduna

Mutane 2 sun mutu a wani sabon hari da aka kai Zangon Kataf, Kaduna

Tsaro
Rhotanni daga jihar Kaduna na cewa mutane 2 ne suka mutu sanadiyyar wani sabon hari da ake zargin Fulani da kaiwa a Zangon Kataf, Jiya, Juma'a.   Kungiyar 'yan Kudancin Kaduna ta SOKAPU ta bayyana cewa maharan sun shiga kauyen Zaman Dabo dake karkashin masarautar Atyap, Zangon kataf inda suka bankawa gidaje wuta. Kakakin kungiyar,  Luka Banniyat yace mutane 2 sun kone kurmus a harin ta yanda ba za'a iya gane su ba. Wanda suka mutu din sune, Cecilia Ishaya, sai Iliya Sunday, daukin gaggawa da sojojin rundunar Operation Safe Heaven suka kai ya dakatar da harin.   Ya kuma ce a 8 ga watan Satumba na 2020 wasu matasa sun afka harin kwantan Bauna na Fulanin inda suka kash 1 me suna, Anthony Magaji sannan 2 suka tsere da raunuka.   Yayi kira ga gwamnati dat...
Hotuna wani gawurtaccen me garkuwa da mutane da ‘yansanda suka yi nasarar kamawa a Kaduna

Hotuna wani gawurtaccen me garkuwa da mutane da ‘yansanda suka yi nasarar kamawa a Kaduna

Tsaro
Wannan hotunan wani gawurtaccen me garkuwa da mutanene da 'yansansa suka yi nasarar kamawa a Kaduna.   DPO din 'yansanda na Narayi, DSP Hamma da hadi Gwiwar 'yan Bigilante suka kamo gawurtaccen me garkuwa da mutanen me suna, Guddal, kamar yanda Trezzyhelm ya ruwaito. A baya, Hutudole ya kawo muku yanda shahararren lauya, Bulama Bukarti ya caccaki Gwamna El-Rufai kan kalaman da yayi akan Kudancin Kaduna  
Duk ma’aikacin asibitin da ya ki zuwa aiki ya yi sallama da aikin kenan>>El-Rufai

Duk ma’aikacin asibitin da ya ki zuwa aiki ya yi sallama da aikin kenan>>El-Rufai

Uncategorized
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi ma’aikatan asibitocin jihar, da ya hada da nas-nas da likitoci cewa duk wanda ya biye wa kungiyar likitoci reshen jihar ya ki zuwa aiki, ya dauka tamkar ya yi sallama da aikin ne Kwata-kwata.     A takarda da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis wanda Muyiwa Adekeye ya saka wa hannu gwamna Nasir El-Rufai ya ce gwamnati ta na dukkan abinda ya Dave domin kula da ma’aikatanta.   ” Kira da a fara yajin aiki a wannan yanayi na Korona, goga wa gwamnati kashin kaji kawai amma Babu dalilin yin haka.     ” Duk ma’aikacin da yake son ya ci gaba da aiki da gwamnatin Kaduna ya je Inda yake aiki ya saka hannu a rajista.     ” Wadanda kuma ba su son yin aikin kada su kuskura su ce za ...
Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta Dokar hana zirga-zirga

Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta Dokar hana zirga-zirga

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana zirga-zirga inda ta bada damar a fita daga karfe 3 na rana zuwa karfe 12 na dare.   Gwamnatin ta kara da cewa sassaucin zai fara aikine daga yau,Laraba zuwa gobe Alhamis inda daga nan kuma za'a kulle sai kuma sati me zuwa inda za'a rika bayar da irin wannan dama daga ranar Talata da Laraba. https://twitter.com/GovKaduna/status/1245343602710061056?s=19 Sanarwar ta kara da cewa an baiwa mutane damane dan su fita su sayi kayan abinci da sauran kayan amfani.
Gaskiya El-Rufai yayi abin yabo,  ‘yan Najeriya ku yi koyi dashi>>PDP

Gaskiya El-Rufai yayi abin yabo, ‘yan Najeriya ku yi koyi dashi>>PDP

Kiwon Lafiya
Wata Alamar siyasa ba da gababa da jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta nuna abin a yabane.   Jam'iyyar ta PDP reshen jihar Kaduna ta jinjinawa gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bisa fitowar da yayi ya bayyana cewa yana dauke da cutar Coronavirus/COVID-19,  ta bayyana wannan abu a matsayin abin bajinta.   Da take magana jiya, Lahadi ta bakin Sakaren jam'iyyar na jihar, Abraham Albera, PDP tace wannan zai karfafawa masu dauke da cutar a jihar suma su fito su bayyana ba tare da fargababa komkuma wanda ake zargin suna da ita, hakan zai sa su kai kansu a gwadasu.   PDP ta kara da cewa tana fatan Allah ya baiwa Gwamnan lafiya cikin gaggawa.   PDP ta kara da cewa tana jawo hankalin jama'ar jihar dasu yiwa dokar zama a gida biyayya dan dakile y...