
COVID-19: Gwamna ganduje ya zabtare al’bashin masu rike da mukamin siyasa da kashi 50
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce duk masu rike da mukaman siyasa za su karbi rabin albashi nan take daga wannan watan na Mayu.
Ganduje ya ce wannan ya faru ne sakamakon gazawar asusun tarayya da kuma samun gibi na kudaden shigar da jihar ke samu a sakamakon kalubalan da ake fuskanta game da cutar coronavirus.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi takaicin cewa “Sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya wanda hakan ya sanya tattalin arziki cikin mashshs-shara, daga karshe ya haifar da mummunan rauni a asusun tarayya ga jihohi, hakan ne ya sanya jihar daukan wannan mataki na zabatare albashin duk masu rike da mukaman siyasa da kashi 50. "
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamna Abba Anwar ya sanar a ranar Lahadi.
...